Mutum Ɗaya Ya Rasu, An Sace Ɗaya a Harin da Aka Kai Lakwaya a Kano; Shugaban Karamar Hukumar Ya Yi Ta’aziyya
By Edita
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari da daddare a Unguwar Lakwaya da ke Kauyen Kururawa, a cikin Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano, inda suka kashe mutum ɗaya suka kuma sace wani.
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
A cewar mazauna yankin, maharan sun shiga garin ne cikin duhu a ranar Lahadi suka fara harbi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya. Haka kuma sun yi awon gaba da Alhaji Yakubu na Tsohuwa Kururawa, abin da ya jefa jama’a cikin tsoro da fargaba.
Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, ya jagoranci tawaga zuwa yankin domin yin ta’aziyya ga mutanen Lakwaya.
Rundunar Ƴan sanda ta Hana Goyo a Babur a Kano
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa labarai na Karamar Hukumar Gwarzo, Auwalu Musa Yola, ya sanya wa hannu, Dr. Mani ya bayyana bakin cikinsa kan wannan mummunar al’amari, tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa Karamar Hukumar Gwarzo za ta ƙara kaimi wajen tabbatar da tsaro da ɗaukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Read also: Shugaban Hukumar KAROTA Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya, Reshen Kano.
Shugaban karamar hukumar ya samu rakiyar mambobin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Sakatare na Karamar Hukuma da mataimakinsa, da DPO da jami’an DSS, da Hukumar Shige da Fice, Civil Defence, da sauran shugabannin hukumomin tsaro.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an ɗauki ƙarin matakai, ciki har da ƙara yawan sintiri da tattara bayanan sirri, domin hana sake faruwar irin wannan hari. Sun kuma shawarci jama’a su kasance masu lura su kuma rika ba da rahoton duk wani abin da suka ga yana da basu gane ba.
Fati, ɗiyar Alhaji Yakubu da aka sace, ta ba da labarin yadda maharan suka kutsa cikin gidansu suka tafi da mahaifinta. Ta roƙi hukumomi da su ƙara jajircewa wajen ganin an kubutar da shi lafiya.
Shugabannin al’umma sun nuna godiyarsu ga ziyarar gaggawa da shugaban karamar hukumar ya kai, suna mai cewa hakan ya karfafa musu gwiwa a wannan mawuyacin lokaci.
Ma’aikatar Ilimi ta Kano Ta Ayyana Ranar Hutu Na Zangon Karatu Na Farko
Dr. Mani Tsoho ya yi addu’ar samun rahamar Allah ga mamacin da kuma alƙawarin kubutar da Alhaji Yakubu cikin koshin lafiya. Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da daukacin al’ummar Lakwaya.



























