Mai martaba Sarki Sanusi ya umarci Hakimai Su Daura Sidi Domin Hawan Babbar Sallah
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya umarci daukacin Hakimai da ‘Yan Majalisar Sarki da su daura damar domin fara shirye-shiryen bikin hawan Sallah-Babba da aka saba bisa al’ada.
Sanarwar da ta fito daga Majalisar Masarautar Kano a wata takarda mai dauke da sahannun, Alhaji Abba Yusuf Danmakwayon Kano, tana umarnin ga dukkan Hakimai da ‘Yan Majalisa na masarautar da su hallara a Birnin Kano domin halartar bikin hawan Babbar Sallah da za a gudanar cikin makon gobe.
“An bukaci Hakimai da sauran shugabannin gargajiya da su iso Kano tare da dawakan su da mahayan su a ranar Laraba, 8 ga Dhul Hijjah, 1446 Hijira, wanda ya yi daidai da 4 ga Yuni, 2025”.
A Iya Karanta Wanna:Hukumar Wasan Dambe ta Duniya Ta Wajabta gwajin jinsi Ga dukkan ‘Yan Wasan
Read also: Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama
Bayan haka, ana sa ran za su halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah, wato 5 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 11:00 na safe, domin karbar umarni da bayani kai tsaye daga Sarkin Kano. Daga nan kuma za a gudanar da wani taro da Hakimai a dakin taron Majalisar Masarauta dake Kofar Kudu, inda za a fayyace tsarin gudanar da hawan Babbar Sallah na bana.

Majalisar ta kuma tabbatar da cewa an tuntubi shugabannin kananan hukumomi domin saukaka shigowar Hakiman daga yankunansu zuwa Birnin Kano.
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
A Iya Karanta Wanna:Kungiyar RATTAWU Reshen Jahar Kano na Ta’aziya Ga ‘Yan Wasan da Suka rasu Sanadiyar Haɗarin Mota
A karshe, majalisar ta roki Allah da ya sanya a gudanar da bikin Babbar Sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.




























