Kungiyar RATTAWU Reshen Jahar Kano na Miƙa Ta’aziya Ga ‘Yan Wasan da Suka rasu Sanadiyar Haɗarin Mota
Ƙungiyar ma’aikatan Radio da Talbijin da Raya Al’adu ta ƙasa reshen jahar Kano (RATTAWU) ta baiyyana kaɗuwar ta da rasuwar wasu daga cikin ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na jaha bisa rasuwar mutum 22 daga cikin su sakamakon mummunan haɗarin mota daya rutsa da su akan hanyar su ta shigowa kano daga jahar Ogun bayan hallartar wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasa.
Read also: Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
A Iya Karanta Wanna:WADANNAN SUNE SUNAYEN YAN WASAN JAHAR KANO 22 DA SUKA RASU A HADARIN MOTA A DAKATSALLE
Shugaban ƙungiyar ta Kano, Babangida Mamuda Biyamusu shi ya sanar da hakan a wata sanarwar da ya bawa manema labarai ciki har da kafar yaɗa labarai ta STENTORNEWS a safiyar yau Litinin.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen jahar Kano Comrade ya sawa hannu ya baiyyana matasan a matsayin zakakurai kuma “yan kishin jahar kano da ƙasa baki ɗaya, wanda tarihin kano ba zai taɓa mantawa dasu ba.
Kwamarade Babangida Biyamusu ya miƙa alhinin sa da kuma daukacin “ya’yan kungiyar ta RATTAWU da wannan babban rashi da akai tare da addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ya gafarta musu yasa Aljannatul-Firdausi ce makomar su ya kuma baiwa iyalan su hakurin jure rashin ya kuma tashi kafadun waɗanda suka jikkata.
Read also: Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
A Iya Karanta Wanna:Hukumar Wasan Dambe ta Duniya Ta Wajabta gwajin jinsi Ga dukkan ‘Yan Wasan
Haka zalika sanarwar tana miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnan kano da Mai martaba sarkin kano II da Ma’aikatar Matasa da Wasanni da ma al’ummar jahar Kano baki daya.




























