Hukumar Wasan Dambe ta Duniya Ta Wajabta gwajin jinsi Ga dukkan ‘Yan Wasan
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Ansamu Koma Bayan ‘Yancin Gudanar Da Aikin Jarida a Faɗin Duniya A Shekaru 5 – Rahoton IEAD
Hukumar wasan dambe ta Olympics ta ce zata fito da gwajin jinsi ga ‘yan wasan dambe domin samun daidaito da aminci. Sanarwar ta mayar da hankali ne kai tsaye kan zakaran Olympic ta Aljeriya, Imane Khelif.
‘Yar dambe Imane Khelif ta rike tutar Algeria a cikin da’irar filin wasa bayan nasarar da ta samu a gasar ajin mata a gasar Olympics ta Paris 2024. Imane Khelif ta zama abar kwatance bayan da ta lashe zinare a gasar damben ajin mata na shekarar 2024 na olympic.
Hukumar wasan Damben Duniya ta sanar da haka a ranar Juma’a tare da fara gwajin jinsi na tilas ga ‘yandambe maza da mata da ke son shiga gasar da ake ɗaukar nauyinsu.
“Gabatar da gwaje-gwaje na wajibi zai kasance wani ɓangare na sabon manufar sanin tabbatar da sanin ‘ jinsi’ da shekaru da nauyi don tabbatar da lafiyar dukkan ‘yan damben da kuma samar da filin wasa na gasake ga maza da mata,” in ji hukumar wasan dambe t duniya a cikin wata sanarwa.
A Iya Karanta Wanna:Sojojin Najeriya sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 60 a Borno
Hukumar ta ce ta yanke wannan shawarar ne biyo bayan cece-kuce da ta taso, da dai sauransu, sakamakon ‘yar damben boksin ta ƙasar Aljeriya, Imane Khelif a gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a bazarar da ta gabata.
A yayin zagayen bugun ƙarshe da aka gabatar tsakanin ta da ‘yar wasan damben ƙasar Italiya da ke adawa da Khelif ta yi ikirarin cewa Khelif ba mace ba ce, saboda ta ji bugun da bata taba ji ba domin ta doku sosai. A inda Imane ta ci gaba da murna da nasarar da ta samu.
Hukumar damben duniya da kwamitin Olympics na kasa da kasa (IOC) ya bukaci shirya gasar damben da za a yi a gasar Olympics ta Los Angeles a shekarar 2028 mai zuwa, ta ce ta sanar da hukumar wasannin dambe ta ƙasar Aljeriya cewa, dole ne Khelif ta mika kanta ga gwajin jinsi kafin a ba ta damar shiga gasar cin kofin ‘Eindhoven Boxing’ da za a yi a Netherlands daga 5 zuwa 10 ga watan Yuni.
“Hukumar dambe ta duniya ta rubutawa hukumar damben boksin ta Aljeriya domin sanar da ita cewa ba za a bar Imane Khelif ta shiga gasar cin kofin na ‘Eindhoven’ ko kuma duk wani wasan dambe na duniya ba, har sai an yi mata gwajin jinsi”.
Za a bukaci kungiyoyin wasan dambe na kasa su gwada ta kuma su tabbatar da nauyin jinsin kowane ne ɗan wasa da kuma ba da takardar shedar shiga gasar dambe ta duniya kafin a ba su damar shiga gasar.
Ta yaya gwajin jinsin zai yi aiki? Sabuwar manufar za ta buƙaci duk ‘yan wasa sama da 18 don yin gwajin ƙwayar cuta ta ‘polymerase chain reaction’ (PCR), kafin a bar su su shiga cikin abubuwan da aka amince da su a damben duniya.
A Iya Karanta Wanna:DA DUMI DUMI:Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traoré, ya Sake Tsallake Harin Yan ta’adda
Ana gudanar da gwaje-gwajen ne ta hanci ko baki, ko kuma ta jini ko kuma yawu, domin a gano takamaiman abubuwan da ke tattare da kwayoyin halitta don sanin jinsin mutum.
“Gwajin PCR wata fasaha ce ta dakin gwaje-gwaje da ake amfani da ita don gano takamaiman kwayoyin halitta, a wannan yanayin SRY gene, wanda ke nuna kasancewar Y chromosome, wanda ke nuna alamar jinsi na halitta,” in ji Hukumar Dambe ta duniya.
Hukumar damben duniya ta ce ‘yan wasan da ke neman yin gasa a nau’ikan mata zar “za a miƙa su ga kwararrun likitoci masu zaman kansu don tantance ƙwayoyin halitta, bayanan gwajin jikin mutum ko wasu bayanan endocrin ta kwararrun likitoci,” idan sakamakon gwajin farko ya nuna shaidar kayan chromosomal na maza.
Sabuwar manufar kuma ta ba da damar daukaka kara.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Imane Khelif ta bayyana shirinta na kare kambunta na zinare a gasar Olympics ta Los Angeles 2028 kuma ana sa ran za ta koma gasar kasa da kasa a Eindhoven mako mai zuwa.
“A gare ni, ina ganin kaina a matsayin mace, kamar kowace mace. An haife ni mace, na tashi a matsayin mace, kuma ina yin rayuwata a matsayin diya,” in ji Imane.




























