An Chanjawa Sanata Natasha Sabuwar Kujerar zama a zauren Majalisar dattijai.
Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, a yau Larabar ta isa zauren majalisar dattijai tare da mijinta yayin da aka dawo zaman majalisar bayan hutun mako guda.
Cikin dan kankanin lokaci da shigar ta zauren Majalisar sai shewa ta barke tare da nuna kauna, mijin kuma ya sumbance ta kafin ta wuce cikin zauran majalisar (chamber) ta zauna.
Sanatan ta jihar Kogi an maye mata gurbin tsohuwar kujarar ta ne da sabuwar kujerar da aka ba ta, wadda ke ci gaba da jawo cece-kuce.
A Karanta Wanna:Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Idan za a tuna rikicin kujerar dai ya janyo cece-kuce ne a majalisar dattawan inda har Sanatar ta zargi shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio da kokarin hakkemata.
Shugaban Majalisar Dattawan dai ya yi watsi da wannan zargi tare da musanta aikata wani laifi. Sai dai wannan zargi da cece-kuce ya haifar da sabbin damuwa game da daraja da kuma halayya a cikin majalisar.
A halin yanzu tuni ‘yan kungiyoyin rajin kare dan adam daban-dabam sukai tsinke zuwa Kofar majalisar dattawan dauke da kwalaye na kiran shugaban majalisar da ake zargi da ya gaggauta sauka daga kujerarsa domin bayar da damar a yi bincike game da abin kunyar da ake zargin ya tabka na kokarin neman Sanata Natashi da lalata.
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
A Karanta Wanna:Addu’ar Magabata ita ce Sirin Samun Zaman Lafiya a Mararabar Gurku, Inji Sarkin Hausawa Mani
A wani bangaren kuma Sanatar mai wakilatar Kogi ta gabatar da korafin ta a rubuce domin majalisa ta hanyarta yin bincike game da abin da ya faru na cin zarafi da shugaban majalisar yai yunkurin yi mata.




























