Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Tsadar Rayuwa: Akpabio Ya Fasa Ƙwai, “Kowace Jiha Ta Samu Naira Biliyan 30 Domin Magance Hauhawar Farashi”

Akpabio
Akpabio

Daga wakilinmu

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya fallasa gwamnonin jihohi, inda ya bayyana cewa kowanen su ya karbi naira bilyan 30 daga Asusun Tarayya domin ya yayyafa wa hauhawar farashi da tsadar kayan abinci a jihohin su ruwa.

Yayin da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an saki naira bilyan 2 ga gwamnoni daga cikin bashin naira bilyan 5 da ta yi bawa kowace jiha a matsayin kudin-goro domin rage tasirin cire tallafin man fetur, Akpabio ya ce bayanan da ke akwai a wurin sa sun nuna cewa an tura musu karin naira bilyan 30 ta hannun Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Cikin Gida (FIRS).

Ka karanta wanna:Tsadar Rayuwa: “Ku Fito Da Kayan Abinci, Ko Mu Farke Rumbunan Mu Siyarwa Da Jama’a”, Inji Muhyi Rimin Gado

Sai dai, ya shawarci gwamnonin da su yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar da suka kamata don rage tsadar kayan abinci da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.

“Mun yi imanin cewa ya kamata kowace gwamnatin jiha ta yi amfani da kuɗaɗen da aka samu wajen tabbatar da cewa ana samun abinci a kasar. Don haka, gwamnatocin jihohi suna da abubuwa da yawa da za su yi. Sun fi kusa da jama’a, kuma ba na son na ambaci ƙananan hukumomi saboda yawancin ƙananan hukumomi gwamnonin jihohi ne ke riƙe da akalar su.

Ka karanta wanna: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa a Kano ta Rufe Runbuna Ɓoye Kayan Abinci

“Imani na shi ne idan gwamnatin jiha ta yi abin da ake buƙata, to ƙaramar hukuma za ta shiga cikin rabon, domin tabbatar da cewa waɗannan abubuwa sun samu jama’a. Amma magana ta gaskiya, bai kamata mu yi watsi da gaskiyar cewa ƴan Najeriya ba labari suke buƙata ba.

Ka karanta wanna:UNICEF Ta Ce Yaro Ɗaya Na Mutuwa Daga Cikin 10 Sakamakon Rashin Tsaftattacen Makewayi

“Ƴan Najeriya na son ganin an ɗauki mataki. Ƴan Najeriya na son cin abinci, kuma za mu samar musu da abinci, babu wani uzuri. Domn abin a bayyane yake,” in ji Akpabio.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...