Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Tsadar Rayuwa: “Ku Fito Da Kayan Abinci, Ko Mu Farke Rumbunan Mu Siyarwa Da Jama’a”, Inji Muhyi Rimin Gado

Muhyi
Muhyi

Daga Wakilinmu

Shugaban hukumar karbar korafe- korafe da yaki da cin hanci da Rashawa ta jihar Kano Batista Muhyi Magaji Rimin Gado ya gargaɗi ƴan kasuwa ko su fito da kayan abincin da suka jibge a rumbuna ko kuma hukumarsa ta fara Kai ziyara runbunan ajiyar Kayan Abinci domin sayarwa da jama’a.

Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace Haramin ne Kuma karya dokar kasa ne boye abinci a lokacin da ake tsanananin buƙatar sa a kasa .

“Za mu je mu buɗe rumbunan kayan Abinci da aka boye, mu sayarwa da jama’a, domin haramun ikata hakan kuma dokar ƙasa tai Allah-wadai da aikata hakan musamman ma a lokacin da ake tsanananin wahalar abinci”.

Muhyi Magaji, ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai, ya ce za a fara Kai simame wuraren da ake zargi an boye kayan abinci kafin watan Azumin Ramadan.

Rimin Gado ya ce wajen da zasu fara dira shine Kasuwar Dawanau inda ya ce duk wanda aka kama ya boye abinci za a fito da abincin a kaishi kasuwa, wanda hakan zai taimaka wajen raguwar tashin farashin da kayan abinci su kai anan jihar kano.

Shugaban ya ce dokar ƙasa ta bashi dama ko dai ya fitar da kayan da aka boye zuwa kasuwa a sayar ko ya kulle rumbun ajiyar Kayan abincin ya tafi Kotu.

Al’umma suna ta kokawa da masifar tsadar kayan abinci wanda ba a taɓa ganin irinsa ba musamman a jihohin arewa. Mutane tuni har sun fara zanga-zanga a jihohin Niger da Kano da sauran wurare domin halkantar da mahukunta su kalli lamarin da idon basira ko a samu sauƙi.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Tsadar Rayuwa: Akpabio Ya Fasa Ƙwai, "Kowace Jiha Ta Samu Naira Biliyan 30 Domin Magance Hauhawar Farashi" - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...