Sahihin Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ
Daga Sunusi K/ Naisa
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida na Ƙasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya, ya ce ba da fifiko ga gaskiya da sahihancin labarai da bin ƙa’idojin aikin jarida shi ke tabbatar da amincewar jama’a, ba wai saurin wallafa labari ba.
Shugaban na NUJ ya bayyana haka ne da yake jawabi yayin ƙaddamar da reshen ‘yan jaridu na yanar gizo-gizo (Online Media Chapel) a Jihar Kigawa wanda aka gudanar a ranar Talata a Cibiyar ‘Yan Jarida (NUJ) da ke Dutse.
Kwamrade Yahaya wanda ya samu wakilcin mai kuɗa da Shiyyar (A), Kwamared Abbas Ibrahim, ya jaddada buƙatar ‘yan jaridun yanar gizo da su tabbatar suna kiyaye wa da duk ƙa’idojin aikin jarida domin kaucewa faɗawa hukunci tare da samun ɗaukaka da kuma amincewar jama’a a ko da yaushe ga labaran da suke wallafawa.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
Kwamrade Yahaya ya taya shugabanni da mambobin sabon Chapel ɗin murnar cika dukkan sharuddan da kudin tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewarsu wajen inganta aikin jarida da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ‘yan jarida.
A cewarsa, ci gaban fasahar zamani ya sauya yadda ake gudanar da aikin jarida, inda kafafen yanar gizo suka zama muhimman hanyoyin yaɗa labarai, wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Read also: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR BAUCHI TA SAURARI RA’AYOYIN JAMA’A GAME DA KIRKIRO SABBIN MASARAUTU
An Gargadi Ƴan Jaridar Yanar Gizo Da Suyi Aiki da Kwarewa Tare da Ƙare Martabar Kasa
Ya ce kafafen yanar gizo suna bai wa ‘yan jarida damar isar da labarai da rahotanni cikin hanzarin ga masu karatu a sassa daban-daban na duniya, tare da amfani da hotuna da bidiyo da sauti da kuma sauran dabarun zamani wajen gabatar da labarai har kan gadon mai karatu.
Sai dai Shugaban ya yi gargaɗi ga ‘yan jaridar cewa waɗannan damammaki na zuwa ne tare da ƙalubale, ciki har da yaɗuwar labaran ƙarya da waɗanda ba a tantance ba, da satar ayyukan wasu da kuma matsin lambar wallafa labarai cikin gaggawa ba tare da cikakken bincike ba.
Ya ce, “A matsayinku na mambobin NUJ, ku zama jakadu na yaɗa gaskiya da riƙon amana. Ku tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin wallafawa, ku mutunta mutunci da sirrin jama’a, ku guji kalaman ƙiyayya, sannan ku tabbatar da cewa adalci, daidaito da ingantaccen rahoto su ne ginshiƙan aikinku.”
Ya ƙara da cewa makomar aikin jarida ta yanar gizo za ta dogara ne da yadda masu sana’ar za su kiyaye ƙa’idojin aiki da kuma kare amincewar da jama’a suka ɗora musu.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa Sakatariyar Ƙasa ta NUJ za ta ci gaba da shirya horaswa da sauran shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar ‘yan jaridun yanar gizo domin tabbatar da cewa aikin jarida na dijital a Najeriya ya kasance abin koyi a matakin ƙasa da ƙasa.
Ya kuma buƙaci mambobin sabon chapel ɗin da su kasance masu haɗin kai, su kare ‘yancin aikin jarida, su rungumi ɗa’a da ƙwarewa, tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa ta hanyar wallafa sahihan labarai masu amfani ga al’umma.
BANKWANA GA MARIGAYI HAZIKIN ‘DAN JARIDA, KWAMARED ALIYU ABUBAKAR GETSO: RAYUWA TA HIDDIMA, TAWALI’U DA SADAUKARWA
A halin yanzu Jihar Jigawa ta biyu bayan wasu jihohin ƙasar nan na ƙaddamar da Online Media Chapel wanda shi ke tabbatar da kasancewar su cikin hadaddiyar kungiyar ‘yan jaridu na ƙasa, NUJ, wanda ake sa ran zai ƙara bunƙasa aikin jarida na yanar gizo a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.




























