Daga Wakilinmu
Hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta rufe rumbunan adana abinci guda 10 da ke ɗauke da kayan abinci a yankin Dawanau da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Shugaban hukumar, Muhyi Magaji ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan rufe rumbunan da ke kasuwar saida Hatsi ta Dawanau da Singer, da kuma Kasuwar kantin Kwari a ranar Lahadi.
Ya ce yawanci ba a sami masu wuraren ɓoye kayan abincin ba, amma waɗanda aka buɗe ɗin cike suke da kayayyaki, waɗanda suka haɗa da taliya da shinkafa da sukari, da sauran muhimman kayyaki.
Ya ce, “Muna sanar da masu mallakar kayan da su kai kansu ga hukumar don fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotu bisa aikata ayyukan da suka saɓa wa doka.
“Kamar yadda kuke gani, hukumar ta cika alƙawarin da ta yi cewa za mu fara yaƙi da ɓoye muhimman kayayyaki a jihar nan.
“Mun fara ne a ranar Alhamis da ta gabata, kuma mun yi tasiri sosai wajen dakatar da hauhawar farashin kayayyaki masu mahimmanci nan take.
“Irin haka ne a cikin mako ɗaya, buhun shinkafa ta yi tsalle daga naira 52,000 zuwa naira 61,000.
Read also: Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli
“Daga abin da muka yi zuwa yanzu, mun tabbata cewa akwai tasiri. Daga nan, za mu je kasuwa domin tabbatar da halin da ake ciki.
“Na farko, mun sami damar dakatar da ƙarin farashin kayayyaki nan take, na biyu kuma, muna da imanin cewa idan muka ci gaba da gwajin, za mu iya saukar da farashin daga inda suka ƙai shi.
“Kamar yadda kuke gani a yanzu, muna duba wuraren ajiyar, kuma mun haɗu da batutuwa da dama waɗanda bayan mun koma ofis, za mu yi taza da tsifa.
“Wata babbar matsala ita ce kowane shago da muka shiga za su yi iƙirarin cewa ma’ajiyar ta World Food Programme ne.
“ Muna mamaki Hukumar samar da abinci ta duniya ( World Food Programme), yadda zata taɓar da ƙasa ta hanyar kwashe abincinta, kuma ta kai wasu ƙasashe baya ga tsananin buƙatar abinci a wannan ƙasa.
“Ka ga kenan, an shaida min a nan yau cewa farashin buhun masara ya yi tashin gwaron zabi daga naira 30,000 zuwa naira 60,000. Don haka ka ga an samu ƙarin kashi 100, wannan ba abin yarda ba ne.
“Za ka iya ganin waɗannan shagunan, akwai ɗaruruwan kayayyaki da suka kai ɗaruruwan miliyoyin naira inda aka ɓoye jibge domin farshinsu ya hauhawa.
Read also: Hukumar NDLEA ta Gano Maboyar Miyagun Kwayoyi a Ƙarƙashin Ƙasa a Kano
“Mun sa muƙullai mun ƙulle shagunan a yanzu, kuma za mu ci gaba da bibiya tare da kame duk masu aikata hakan, domin ba za mu ƙyale su ba”. Inji Muhuyi.
Rimin Gado ya ce wannan ba kasuwan ci ba ne, ɓoye kaya ne. ” Don haka mun zaburar da ƙwararrun ma’aikatanmu domin su ci gaba da binciken inda ake ɓoye kayyaki muhimmai don a tsawalawa jama’a tare da kawo mana rahoto.”




























