Daga Wakilinmu
Mazauna Kano sun nuna damuwa kan sakin Murja Ibrahim Kunya ƴar Tik tok daga cibiyar gyara hali ba tare da sun jin sharuɗɗan bada beli ko kuma daɗiɗin sakinta ba.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Idan an tuna, jami’an hukumar Hisba ta jihar Kano ne suka kama mashahuriyar ƴar TikToker sakamakon zargin da ake yi na saka bidiyon baɗala a shafinta na sada zumunta, wanda ake ganin ya saba wa tanade-tanaden shari’ar musulunci ta jihar Kano ta shekarar 2000.
Mai magana da yawun hukumar Hisbah ta Kano, Malam Lawal Ibrahim Fagge, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an kama Kunya ne bayan da suka samu korafe-korafe daga makwabtanta da kuma ci gaba da aikata mummunar ɗabi’arta na yaɗa baɗala da take yi ta kafar TikToker a cikin al’umma.
Ka Karanta wanna: Shaharrariyar Ƴar Tiktok Murja Kunya Ta Faɗa Komar Hisbah A Kano
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Daga bisani kotun Shari’ah ta jihar Kano karkashin jagorancin Malam Nura Yusuf Ahmed ta tura ta gidan gyaran hali, na tsawon mako guda a tashi farko, amma daga a halin yanzu akai tsinkayen an sake ta ba tare da jama’a sun ji sharuddan sakin nata daga gidan gyaran halin ba.

Murja Kunya a hukumar hisbah ta jihar Kano.
Wannan al’amari ya jawo martani da ce-ce-kuce a faɗin jihar Kano.
Da aka tuntuɓe shi, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar gyara hali ta Najeriya, na Kano, SC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya tabbatar da cewa an saki wacce aka tsaren a halin yanzu, yana mai bayyana cewa ana kawo fursunonin gidan gyaran hali bisa umarnin kotu kuma ana sakin su bisa umarnin na kotu.
Ka karanta wanna: Ko Ka San Burushin Wanke Haƙora Na Iya Tasiri Ga Lafiyar Baki Da Jikin Dan Adam?
Kokarin samun bayanai daga Muzammil Ado Fagge, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Sashen Kotun Shari’ah ta Jihar Kano, dangane da sharuddan belin ko kuma dalilan da akai amfani da shi na dakatar da shari’ar, hakan ya citura saboda bai amsa kira wayar da akai masa ba daga wakilin mu.
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Ka karanta wanna: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa a Kano ta Rufe Runbuna Ɓoye Kayan Abinci
Barista MM Isa, wani mai lauya ne a Kano, ya jaddada cewa ikon bayar da belin na da alaƙa da kotu, yana mai jaddada wajibcin yin amfani da wannan karfin, musamman a shari’o’in da laifin da ake zargi zai iya yin mummunan tasiri ga al’umma.




























