Daga Wakilinmu
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama Murja Ibrahim Kunya, fitacciyar ƴar Tiktok da ta yi suna a shafukan sada zumunta na zamani bisa zargin yaɗa baɗala.
Read also: Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano
A safiyar ranar Talata ne wani gidan rediyo a Kano da wasu daga shafukan sada zumunta suka yaɗa rahoton kama Murja Kunya.
Hukumar Hisbah ta nemi damke akalla mashahuran ’yan Tiktok su shida da ake zargi da yada bidiyoyin Baɗala ciki har da Murja, a shafukansu na Tiktok da sauran kafafen sada zumunta na zamani matakin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokokinta.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Idan za’a iya tunawa ko a baya-bayan nan babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gayyaci ɗaukacin mata ‘yan Tikto da ke Kano zuwa wani zama inda hukumar ta yi tayin gyara musu sana’o’i su da kuma basu tallafin karatu domin kyautata rayuwar su.
Bayan waccar gayyata ne sai Murja da sauran abokanta da ake nema ruwa a Jallo suka fitar da wani Bidiyon da Hisbar ta ce ya saɓawa koyarwar Addinin musulunci da kuma al’adar Malam Bahaushe.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Kafar yaɗa labarai ta STENTORNEW ta tuntuɓi mai magana da yawun hukumar hisbah, Malam Lawan Ibrahim Fagge wanda ya tabbatarwa da wakilinmu kamun na Murja a daran jiya litinin.
Lawan fagge ya ce ” Dakarunmu na hisbah sun kama ta da misalin ƙarfe 11 na dare, bayyan saurayinta ya maido ta gida a unguwar Tinshama.
” Ya ce kamun ya na da nasaba da ƙorafi da muka samu daga maƙoftanta baya ga kaucewa yarjejeniyar da mukai da ita da kuma sauran abokan yaɗa baɗalar, kuma zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da ita gaban ƙuɗiya domin ta girbi abin da ta shuka”. Inji kakakin hisbah.





























Pingback: Ƴar Tik Tok Ta Yi Ɓatan Dabo: Al'ummar Kano Na Ce-Ce-Kuce Kan Sharuɗɗan Beli - The StentorNews Hausa
Pingback: Shugaban Kanfanin TikTok Ya Gargaɗi Amurka Kan Haramta Shafin - The StentorNews Hausa