Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62
Daga Adita
Dakarun rundunar Sashi na 2 (Operation FANSAN YAMMA), sun samu sabbin nasarori a yaƙin da ake yi da ta’addanci da fashi da makami a Arewa maso Yamma, inda suka kashe wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, suka ƙwato makamai tare da ceto dabbobi da dama da aka sace a jihohin Sokoto da Katsina.
Read also: Sojoji Sun Daƙile Hari Yan Bindiga A Kano
An gudanar da waɗannan samame ne a ci gaba da hare-haren soji kan masu aikata laifuka a ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto da kuma ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 8 (Division da Sector 2 Operation FANSAN YAMMA), Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
A cewarsa, dakarun sun yi gaggawar kai ɗauki bayan samun bayanan sirri kan wani yunƙurin ƙona ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice na Najeriya da ke ƙauyen Ruwa Wuri a ƙaramar hukumar Tangaza, wanda ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne suka shirya.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Osoba ya ce dakarun sun fafata da maharan a musayar wuta mai ƙarfi, inda suka kashe biyu daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere sakamakon ƙarfin wutar da sojojin suka yi musu.
“Bayan artabun, dakarun sun gudanar da sintiri a yankin tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, alburusai, da kuma babur da ake zargin maharan sun yi amfani da shi,” in ji shi.
A wani samame daban kuma, dakarun da ke sintiri a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina sun yi arangama da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne da ke tafiya da dabbobin da suka sace a yankin Danya Bakwai.
Bayan musayar wuta, dakarun sun tilasta wa maharan tserewa tare da barin dabbobi 62 da suka sace, waɗanda daga bisani aka mayar wa masu su a fadar Hakimin Daddara da ke Jibia.
Read also: Sojoji Sun Kifar da Gwamnatin Shugaba Ƙasar Benin Patrice Talon
Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Bulla A Nijeriya
Rundunar sojin ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri a kan lokaci.





























Pingback: Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya - The StentorNews Hausa