Kishin Bunƙasar Kano Shi Yasa Gwamna Yusuf Ya Yi Sauyin Sheka – NNPP
Daga Yazid Sunusi
Read also: Majalisar Dokokin Kano ta goyi bayan Gwamna Yusuf Ya fita Daga Jam’iyyar NNPP
Read also: Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ƙarƙashin jagorancin Dr. Boniface Aniebonam ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bar tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar ne saboda abin da ta kira nufin sabuwar bautar siyasa daga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba don wata manufa ta ƙashin kai ba.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa Kwankwaso ne babban mai cin amana a wannan rikici, domin shi ne ya ci amanar wanda ya kafa NNPP, wato Aniebonam, ba Gwamna Yusuf ba. Ta ce duk ƙoƙarin da Yusuf ya yi a matsayinsa na jagoran NNPP a Kano na sasanci da sulhu an ƙi karɓa saboda girman kai da kwaɗayi.
NNPP na martani ne kan kalaman da tsohon Baban Jam’iyya, Elder Buba Galadima, ya yi dangane da sauyin sheƙar Yusuf.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kasa (Arewa maso Yamma), Alhaji Sani Danmasani, ya fitar, jam’iyyar ta ce:
“Ya dace ‘yan uwa da iyalan Kwankwaso da Galadima su shiga tsakani kafin baƙin ciki mai tsanani ya riske su.
Sanarwar ta ce “Wannan kuwa saboda cikakken nazari kan halin da Galadima ya nuna a tashar Arise TV ya nuna cewa akwai alamun matsalar lafiyar kwakwalwa da ka iya tasowa.
“Sauyin sheƙar Yusuf zuwa APC ya shafi Galadima da Kwankwaso matuƙa, har zafin rai da raɗaɗi suke bayyana a cikin maganganunsu.
“Zafin ransu ya kai matakin da idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, zai iya haifar da baƙin ciki mai tsanani. Mai yiwuwa ma waɗannan manyan mutane suna fama da rashin barci.”
A cewar jam’iyyar, abin da ya fi ɗaukar hankali a bayanan Galadima a shirin Arise TV shi ne labarin tafiyarsa ta mota daga filin jirgin saman Enugu zuwa garin Umuawulu a Jihar Anambra, mahaifar wanda ya kafa NNPP, Aniebonam.
“Galadima ya ce ya isa Anambra da ƙarfe 2:00 na dare domin ganawa da Aniebonam, da nufin samo dandalin siyasa ga Kwankwaso da wasu don tunkarar zaɓen 2023.
“Abin mamaki, Yusuf wanda shi ne babban wanda ya amfana daga wannan tafiya mai haɗari zuwa Umuawulu, shi ne ake zargi da cin amanar iyalin NNPP ta hanyar shiga jam’iyyar APC tare da wanda suke kallon a matsayin maƙiyi wato tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a APC, Abdullahi Ganduje.
“Galadima da Kwankwaso da ke kuka da cewa an ci amanarsu, su ne aka bai wa damar amfani da dandalin NNPP kyauta domin yin takara a zaɓen 2023.
“Su ne kuma suka ci amanar Aniebonam, tare da yunƙurin ƙwace jam’iyyar da ya kafa tun 2001. Har yanzu suna ƙoƙarin ƙwace tsarin NNPP ba tare da lamiri ba, amma suna kiran Yusuf da mai cin amana.
“Abin tambaya shi ne, me ya sa Kwankwaso da Buba Galadima ke kuka suna tayar da hankalin al’umma, alhali suna sane cewa Allah yana tafiyar da al’amura ta hanyoyi daban-daban?”
Jam’iyyar ta ƙara da cewa matakin da Yusuf ya ɗauka kariya ce ta kai, domin tsira daga bautar siyasa ta zamani da kuma katsalandan da Kwankwaso ke yi a harkokin mulkin Jihar Kano.
Ta ce maimakon ci gaba da kuka kan Yusuf, ya kamata Kwankwaso da ƙungiyarsa su nemi gafarar Allah tare da neman yafiya daga waɗanda suka ci amanarsu.
Kabilu Mazauna Malam Madori da Ƙaugama Sun Karrama Ɗan Majalisa Tarayya Hon. Makki Yalleman Bisa Kulawa Ga Ilimi
NNPP ta ƙara da cewa tasirin Kwankwaso a siyasar Kano ya ragu ƙwarai, kuma hakan ba zai hana sake zaɓen Gwamna Abba Yusuf a shekarar 2027 ba.



























