Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
Daga Wakilinmu
Read also: Ko Kasan Sabbin Kwamishinonin Da Gwamna Kano Abba Yusuf Ya Naɗa?
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
A cikin fefen bidiyo da Kakakin Gwamna Sanusi Bature Dawaki Tofa ya sanya a shafukan sadarwa, ya ce sanarwar ta tabbatar da fitar Gwamna Abba Yusuf a yau Juma’a, bisa nasaba da rashin jituwar Gwamna da kuma wasu shugabannin jam’iyyar a matakin jihar, da kuma yadda ake tafiyar da wasu muhimman lamura na siyasa.
Read also: Gwamna Abba Yusuf Zai Biya SSA, SA da PA na Zamani Mulkin Ganduje Kuɗaɗen Su
Gwamnan Jihar Kano ya kara da cewa, muradun sa na inganta ci gaban jihar Kano da al’umma ne suka fi muhimmanci a gare shi, kuma yana ficewa domin neman sabbin hanyoyi da zai iya amfani da su wajen gudanar da mulki cikin lumana da haɗin kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyin masu kishin jihar Kano.
Majalisar Dokokin Kano ta goyi bayan Gwamna Yusuf Ya fita Daga Jam’iyyar NNPP
Masana harkokin siyasa a jihar sun bayyana cewa wannan mataki na iya haifar da canje-canje a tsarin siyasar Kano, musamman idan Gwamnan ya shiga wata jam’iyya mai ƙarfi ko kuma ya kafa sabon tsari na siyasa a jihar.
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shiryawa don zabukan 2027, inda wannan mataki na iya jawo sabuwar haɗin kai ko rikice-rikice a tsakanin jam’iyyu masu tasiri a Kano.
Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya
Amma har yanzu Gwamna Abba bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, amma masana siyasa suna zargin Gwamna ka iya koma jam’iyyar APC gani yanda dangantaka take ƙara ƙarfi a tsakanin shugabanni masu mulki a gwamnatin tarayya da jihar Kano.



























