Gwamna Abba Yusuf Zai Biya SSA, SA da PA na Zamani Mulkin Ganduje Kuɗaɗen Su
Daga Sunusi K /Naisa
Read also: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince zai biya tsofaffin Masu baiwa gwamna Shawara na musamman da mataimaka na musamman na zamani mulkin tsohon Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Kuɗaɗen sallamarsu.
Kwamishina Yaɗa labarai da a Al’amuran Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanar da hakan da ya karbi bakunci SSA da SA da PA na mulkin tsohon Gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje, waɗanda suka je ofishinsa domin sanar da shi shirinsu na yiwa Gwamnan Kano maraba zuwa jam’iyyar APC.
“Mun tattauna da gwamnan Kano maganarku , kuma ya ban tabbacin zai biyaku kuɗaɗen sallamarku nan bada jumawa ba , duk da cewa an sanar da shi cewa babu wata doka da ta ce a biyaku kuɗin sallamar”. Ina ji Kwamishina Waiya.
Read also: Ko Kasan Sabbin Kwamishinonin Da Gwamna Kano Abba Yusuf Ya Naɗa?
Ya ce gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarce shi da ya je su tattauna da Sakataren gwamnatin su kuma tsara yadda za a biya kudin .
Kwamishinan Waiya ya kuma ce suna da gado a jam’iyyar APC don haka ya ce in ma sun koma APC ba wani abun mamaki ba ne.
” Mu yanzu gwamna mu ke jira ya bayyana matsayarsa mu kuma za mu mara masa baya domin ya haɗu da sauran ‘yan APC domin ciyar da jihar Kano gaba”.
Da yake nasa jawabin shugaban tawagar Alhaji Gidado Ahmad Satatima ya ce sun shirya tsaf domin yi wa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf maraba zuwa jam’iyyar APC.
Ya ce sun tabbata Gwamnan Abba Mutumin kirki ne da yake da tausayin talakawa kuma ya yiwa jihar Kano aiyukan cigaba, inda ya ba da tabbacin za su haɗa kai da shi don ciyar da jihar Kano gaba.
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Kyautata Zamantakewar Aure: Kungiyar Anwarul-Qalam Bauchi ta Horas da ‘Yan Mata 100
Gidado Satatima ya kuma godewa Gwamnan saboda ƙoƙarin da yake na ganin ya biyasu kuɗaɗen sallamarsu .



























