Rashin Bawa Mata da Kanana Yara Damar Zuwa Asibiti Domin Rigakafi Illa ne Ga Rayuwar Su, In ji Jami’in Lafiya
Daga Sunusi K /Naisa
Read also: Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko
An bayyana rashin bawa mata masu juna biyu da ƙanana yara damar zuwa asibiti a sati don kuda da lafiyar su gami da samun alluran rigakafi ka iya haifar da babbar illa ga rayuwar su.
Jami’in lafiya a matakin farko na karamar hukumar ta Rano, Alhaji Ya’u Musa Durum ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bayyana sakamakon aikin alluran rigakafin cutar shan inna da sauran cuttutuka masu saurin halaka matan da kananan yara na karamar hukumar.
Jami’in ya shawarci magidanta a karamar hukumar Rano da su ci gaba da barin matan su masu ciki da kananan yara suna zuwa asibitoci don alluran rigakafi na sati-sati.
Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus
Wannan na cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labarai na shiyar ta Rano, Abdullahi Musa Gyadi Gyadi ya raba inda jami’in lafiyar a matakin farko ya kara da cewa, rashin zuwa asibitoci don alluran rigakafin yana daga cikin matsalolin da ka haifar da kamuwa da cuttutuka har ma da mace-macen wata masu ciki da kananan yaran.
Alhaji Ya’u Musa Durum ya nuna gamsuwarsa hadin kan masarautar Rano bisa jagorancin Mai martaba Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isah Umaru da Hakimin Rano dama Dagatai da masu unguwannin yankin da sauran masu ruwa da tsaki suke baiwa aikin alluran rigakafin a duk zagaye.
Read also: Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf
Cikin jawabinsa, shugaban karamar hukumar, Alhaji Naziru Ya’u Rano jaddada kudirin majalisar karamar hukumar ya yi na ci gaba da koyi da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf a duk wasu tsare-tsaren ta na ingata lafiyar al’umar yankin.
Shugaban karamar ya yi kira ga al’umar yankin da su ci gaba da addu’o’i ga majalisar karamar hukumar a kokarinta na samar da asibitoci da gyara wadanda ake da su tare da masu da magunguna.
Alhaji Naziru Ya’u Rano ya nuna gamsuwarsa da yadda ma’aikatan lafiyar suke gudanar da
aikin su a yankin tare da fatan za su rubanya kokarin su don bunkasa lafiyar al’umar al’umar karamar hukumar.
A bayanan su, manajan lura da Alluran rigakafin karamar hukumar, Alhaji Musa Muhammad Gora da jami’in ilmantarwa, Alhaji Sabo Uba Gani sun bayyana cewa sama da yara dubu 53,387 aka yiwa alluran rigakafin cutar ta shan inna a wannan zagayen aikin da aka Kamala inda aka baiwa karamar hukumar allurai dubu 53,550.
Read also: Yunwa: Sakamakon Rashin Abinci Mai Gina Jiki Yara Sama da 650 Sun Halaka a Katsina -MSF
Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Ya Saɓawa Doka, In Ji Farfesa Mai Bushira
Sun kuma godewa sun kuma kara da cewa an gudanar da taro da masu rike da sarautu da sauran masu ruwa da tsaki tun farko kafin aiwatarvda aikin alluran rigakafin don cimma nasarar da ake bukata.




























