Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Ma’aikatar Ilimi ta Kano Ta Ayyana Ranar Hutu Na Zangon Karatu Na Farko

Ɗalibai
Ɗalibai

Ma’aikatar Ilimi ta Kano Ta Ayyana Ranar Hutu Na Zangon Karatu Na Farko

Daga Sunusi K/Naisa

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ayyana Asabar, 13 ga Disamba 2025 a matsayin ranar da za a fara hutun zangon farko ga dukkan makarantun kwana da na jeka ka dawo na gwamnati da na masu zaman kansu na firamare da sakandare a fadin jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya wa hannu.

Ana kuma shawartar iyaye da masu kula da dalibai da ɗaliban ‘yan makarantun kwana da su kiyaye da ranar Juma’a 12 ga watan Disamba 2025 domin liban ‘ya’yansu zuwa gida.

Rundunar Ƴan sanda ta Hana Goyo a Babur a Kano

Daliban makarantun kwana za su koma makarantu a ranar Lahadi, 18 ga Janairu 2026, yayin da ɗaliban makarantun yini za su koma a ranar Litinin, 19 ga Janairu 2026.

Zango na biyu zai fara ne a ranar Lahadi, 18 ga Janairu 2026, kuma zai kare a ranar Asabar, 18 ga Afrilu 2026, yayin da zangon na uku zai fara a ranar Lahadi, 3 ga Mayu 2026, kuma ya kare a ranar Asabar, 1 ga Agusta 2026.

A cewar kalandar, ɗalibai za su shafe kwanaki 10 na lokacin azumi a makarantunsu kafin hutun Sallah. Hutun Sallah zai fara ne daga ranar Lahadi, 1 ga Maris 2026, kuma zai kare a ranar Asabar, 21 ga Maris 2026.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi kira ga iyaye da masu kula da ɗalibai da su tabbatar da bin ranakun da aka kayyade.

Rungumar Tsarin Majalisar Wuccin Gadi A Najeriya Na Iya Ajiye Biliyoyin Naira A Shekara, In Ji Ali Ndume

Ya gode wa iyaye da al’ummar jihar bisa goyon baya da haɗin kai da suke baiwa Ma’aikatar, tare da yi wa ɗalibai fatan hutun zangon farko mai inganci da cike da albarka.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...