Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Shugaba Donald Trump Ya Soke Visa Dubu 80 Ta ‘Yan Najeriya Da Wasu Kasashen Waje

Tinubu da Trump
Tinubu da Trump

Shugaba Donald Trump Ya Soke Visa Dubu 80 Ta ‘Yan Najeriya Da Wasu Kasashen Waje
Daga Edita

Gwamnatin Tarayyar Amurka ta soke takardun visa na kusan mutane Dubu Tamanin (80,000) daga kasashen waje, ciki har da wasu ‘yan Najeriya, bayan wani cikakken bincike da aka gudanar kan masu rike da visa da ake zargin suna da hannu a laifuka ko matsalolin tsaro.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, ta bayyana cewa wannan mataki wani bangare ne na ƙudirin gwamnatin  Shugaba Donald Trump tun a zangon mulkinsa na farko na tabbatar da tsaron ‘yan Amurka.

Sanarwar ta bayyana wannan mataki da kalmar “alkawarin da aka yi, alkawarin da aka cika,” tare da jaddada cewa tsohon Shugaba Donald Trump “zai ci gaba da sanya tsaron da muradun al’ummar Amurka a gaba.”

Amurka Na Yunƙurin ƙaƙabawa Gwamnonin Arewacin Najeriya 12 da Alƙalai da Sarakunan Gargajiya Takukumi

A cewar ma’aikatar, mutanen da abin ya shafa sun aikata laifuka daban-daban kamar su cin zarafin mutum (assault) da sata, da kuma tukin mota cikin maye (DUI).

Rahoton ya nuna cewa mutum 16,000 ne aka soke musu visa saboda DUI, 12,000 saboda laifin duka, yayin da 8,000 kuma suka rasa visansu saboda sata.

Haka kuma, an bayyana cewa wasu soke-soken visa sun shafi manyan laifuka irin su ta’addanci, bayar da tallafi ga ayyukan ta’addanci, barazana ga tsaron jama’a, da kuma wuce lokacin da visa ta amince musu da zama.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta jaddada cewa wannan mataki wani ɓangare ne na kokarin gwamnati na kare iyakokin Amurka da tabbatar da gaskiya da tsari a harkar shige da fice.

Ta kuma nanata cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace kan duk wani bako da ke iya zama barazana ga tsaron kasa ko zaman lafiyar jama’a.

Ana Zargin Fashewar Bam A Masallacin Juma’a Yai Sanadiyar Jikata Daruruwan Mutane a Yau

Wannan sabon mataki na soke visa ya sake tabbatar da tsauraran manufofin gwamnatin Trump kan shige da fice da kuma fifita tsaron al’umma fiye da la’akari da diflomasiyya ko siyasa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...