Ana Zargin Fashewar Bam A Masallacin Juma’a Yai Sanadiyar Jikata Daruruwan Mutane a Yau
Daga Wakilinmu
‘Yan sanda a ƙasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar.
Suheri ya ce an kai mutane 54, galibinsu dalibai zuwa asibiti da raunuka masu sauki da masu tsanani, ciki har da wadanda suka kone.
Read also: An Buƙaci Mutane Su Fito Gwajin Hawan Jini da Ciwon Siga
Read also: Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko
Ya kara da cewa mutum 20 na ci gaba da samun kulawa a asibiti, inda uku daga cikinsu ke fama da raunuka masu tsanani.
Haka kuma shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu karfi da misalin karfe 12 na rana a agogon ƙasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a a masallacin.
Kafafen yada labarai na cikin gida a kasar sun nuna bidiyon da ke nuna layin ‘yan sanda da ke kewaye da makarantar, inda motoci masu ɗaukar marasa lafiya ke tsaye a gefe.
Sai dai hotunan masallacin ba su nuna wata mummunar lalacewa ba sakamakon harin.
Kwamishinan ‘yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar.
Aminiya



























