Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
Daga Sunusi K/Na’isa
Wasu Daliban Jami’ar Kimiya da Fasaha ta Aliko Dangote dake Wudil a jihar Kano sun Karrama Manajan Darakta Karota Hon. Faisal Mahmud Kabir da shedar girmawa.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
Daliban wadanda suke Karatun Digiri na ‘part time’ sunyi wannan yunkurin ne ganin irin hidimar da Manajan Daraktan hukumar ta Karota yake yi na tallafawa Ilimi a faɗin Jihar Kano.
Da yake ƙarin bayani shugaban Ƙungiyar ɗaliban Jami’ar Kwamared Ibrahim Shafir Hashim yace wannan ziyara nada nasaba da irin kokarin Shugaban na Karota wajen tallafawa ɗalibai daga makarantu daban-daban.
Kwanared Ibrahim Shafir ya cigaba da cewa MD KAROTA yana Kuma ɗaukar nauyin ɗaliban da har su kammala Karatun su a ciki da wajen Jihar.
“Abinda ya bamu Sha’awa shine yadda Hon. Faisal yake tallawa batare da nuna wata wariya ko banbanci ta akidar siyasa ba, shidai bukatar shi a samu Ilimi.”
Shugaban ɗaliban ya ƙara da cewa suma ma’aikatan hukumar ta Karota ya basu damar dukkan Wanda yake da takardar shedar kammala sakandire kuma yake da bukatar cigaba da karatu daya koma zai tallafa masu.
“Wannan kaɗan ne daga cikin irin ƙoƙarin da yake yi kuma shi ne ya bamu ƙwarin gwuiwa wajen kai masa ziyarar ofishin sa tare da karrama shi.
A nashi jawabin shugaban hukumar ta Karota Hon. Faisal Mahmud Kabir ya fara da nuna farin cikin shi bisa wannan yunƙuri na ɗaliban.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Manajan Daraktan ya tabbatar dacewa wannan ƙoƙarin na ɗaliban yana da matukar tasiri musamman karatun ‘part time’ da yake bakowa yake iyashi ba saboda wasu dalilai na rayuwa.
Ga Wasu Labaran:
- Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar
- BARAYI SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI
- ICPC Ta Kama Dan Jaridar Bisa Zargin Damfara Ta Naira Miliyoyin 14
Hon .Faisal ya bukaci ɗaliban dasu yi tunanin samar da wata kafa da zata taimakawa waɗanda basu samu damar da zasu cigaba da karatu ba suma.
“Wannan karatun da kuke gani kamar gobe ne zaku ga kowa ya kammala shi, saboda shi karatu indai kana yi tare da maida hankali komin dadewa zakaga ka gamashi.
Yace Wannan hukuma a shirye take wajen cigaba da basu goyon baya da dukkanin haɗin kan da suke bukata dan cimma nasarar abinda suka sanya a gaba.
“Kuyi ƙoƙari wajen ƙarfafawa matasa,yan kasuwa da ma’aikata gwuiwa wajen ganin suma sun shigo wannan tsari na karatun ‘part time’ da sauran karatuttuka.
Haka zalika yace dukkan ma’aikatan Karota da suke part time zasuyi Wani tsari da zai taimaka masu wajen samun irin wannan damar.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Yace kamar yadda aka Sani bukatar gwamnatin Jihar Kano a yanzu shine samar da Ilimi ga dukkan Al’ummar ta, Kuma shine matakin farko da Mai girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya Sanya gaba.
Kuma idan Al’umma suka samu ingantaccen Ilimi Kuma sahibi shine zakaga Jama’a na rayuwa kan tafarki Mai Kyau.
Jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada shi ya sanar wa da jaridar The Stentor News Labarin.




























