Daga Sunusi K/Na’isa
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta fitar da gargaɗin kuɗa da lafiyar jama’a dangane da kauce wa kamu da cutar zazzabin Lassa da kuma yiwuwar yaɗuwar a fadin ƙasar nan a wannan lokaci.
Read also: Ƙarin Bayani Akan Tsarin Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA)
Daraktan Janar na cibiyar, Dr. Muhammad Adamu Abbas, ya bayyana cewa wannan gargaɗi ya zama wajibi sakamakon sanarwar gaggawa da suka samu daga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC).
Dr. Abbas ya bayyana cewa sanarwar daga NCDC ta nuna yiyuwar ƙaruwa a haɗarin yaɗuwar cutar Lassa daga watan Oktoba zuwa na Mayu.
Ga Wani Labarin:Gwamnatin Kano Ta Yaba da Nadin Shugabannin Gidajen Rediyo Bisa Cancanta
Ya ce, saboda yanayin muhalli da tsarin rayuwa na Kano, jihar na cikin fargaba na yuwuwar barkewar cutar. Don haka ya shawarci al’umma da su kiyaye tsafta sosai tare da bin matakan kariya.
Sanarwar ta shawarci jama’a da su rika tsaftace muhalli da adana abinci a rufaffun muzubi, da kuma toshe kowanne wuri da beraye za su iya shiga gida.
Read also: Majalisar Dokokin Jihar Kano Zata Tallafawa Hukumar DMCSA Don Ta Cimma Gaci
Ya kara da cewa duk wanda ke fama da zazzabi matsananci kuma bai warke ba, ko wasu alamomin da ke nuna kamuwa da cutar, ya garzaya zuwa asibiti mafi kusa domin samun kulawar kwararrun masana kiwan lafiya cikin gaggawa.
Sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi nan ta ce Gwamnatin Jihar Kano ta buɗe Cibiyar Aikin Gaggawa ta Lafiya (PHEOC) domin tunkarar yaɗuwar cutar Lassa a matsayin matakin rigakafi.
Daraktan Janar ya ce an fara tanadin kayayyakin lafiya da suka haɗa da kayan kariya (PPE), da magungunan antiviral, da kuma horar da ma’aikatan lafiya kan yadda za a kula da masu dauke da cutar da kuma hana yaɗuwar ta.
“Ana kuma gudanar da wayar da kan jama’a da kuma kashe beraye a kananan hukumomin da ke cikin haɗari a matsayin wani bangare na tsarin ‘One Health’ wanda ke haɗa sassan muhalli da noma.”
KNCDC ta roki jama’a da su rinka kai rahoton duk wata alamar cutar cikin hanzarin ta hanyar hanyoyin sa-ido da aka tanada, maimakon gwada magani a gida.
Dr. Abbas ya tabbatar da cewa cutar Lassa tana da matakan kariya da kuma magani idan aka gano ta da wuri, yana mai cewa: “Idan muka haɗa kai, za mu kare Jihar Kano daga yaɗuwar cutar Lassa a wannan lokaci.” inji shi.
Zazzabin Lassa, cuta ce mai hatsari da ke haifar da zubar jini, wadda ke yaɗuwa ta hanyar hulɗa da abinci, ko ruwa, ko kayan gida da aka gurɓata da fitsari ko bayan gidan berayen da ke ɗauke da kwayar cutar.
Read also: Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano
Ga Wani Labarin:BARAYI SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI
Hakanan, cutar na iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar jini ko ruwan jikin masu ɗauke da cutar.
Alamomin cutar Lassa sun haɗa da zazzabi da baya warkewa da ciwon makogwaro da ciwon ƙirji ko ciki da amai da gudawa, da kuma zubar jini daga kowanne bangare na jiki. Masana lafiya sun ce gano cutar da wuri da kuma samun kulawa na da matukar tasiri wajen ceton rai.



























