Daga: Adita
Babbar Kotun Abuja ta tabbatar wa Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa da Dangogin su (ICPC) damar bincike kan zargin badaƙala a harkar tallafi karatu na jihar Kano. Haka kuma kotun ta kori ƙarar nan take.
Read also: Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar
A baya dai wasu jami’en gwamnatin jihar Kano su suka shigar da ƙarar a gaban babban kotun bisa rokon kotun ta haramtawa ICPC damar binciken zargin badaƙalar tallafin karatun.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, wanda Daraktan Wayar da kan Jama’a na hukumar ICPC, ya sawa hannu, Mr. Demola Bakare, fsi, ya ce ICPC ta ce batun binciken ya zo ne sakamakon wani korafi da aka kai mata, ana zargin badaƙalar kuɗaɗen tallafin karatu na jihar Kano.
A sanarwar, kotun ta ce bayan karɓar ƙorafin, ta gayyaci jami’ai a ma’aikatar ilimi mai zurfi da kuma ma’aikatar harkokin tallafin karatu na jihar Kano domin su bada bayanai da kuma takardu akan zargin.
Read also: Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 3 A Gidan Gyaran Hali Sakamakon Kona Taya A Kano
Ga Wani Labarin:Ƙungiyar likitoci ta janye yajin aikin gargaɗin da ta fara
Sai dai mai makon su amsa gayyatar da aka yi musu, sai jami’an, ƙarƙashin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Dakta Hadi Bala, suka garzaya kotun tare da shigar da ƙara mai lamba 2857/2025 akan Antoni Janar na Ƙasa da ICPC, suna ƙalubalantar gayyatar da akai musu da cewa an take musu haƙƙi a matsayin su na ƴan ƙasa.
Da yake yanke hukunci akan ƙarar, Alƙalin kotun, Mai Shari’a Obanor ya umarci a ƙara suna jami’an hukumar tallafin karatu ta Kano a cikin ƙarar sannan a cire Antoni Janar na Ƙasa daga ƙarar.
Alƙalin ya kuma ce takardar gayyatar da ICPC ta aike wa jami’an na gwamnatin Kano ta na nan a kan doka kuma ba a take haƙƙin su na ƴan ƙasa ba.
Read also: Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Ga Wani Labarin:Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo
Daga karshe ICPC ta ce Alƙalin ya kori ƙarar saboda rashin ingancin ta.




























