Connect with us

Hi, what are you looking for?

KASUWANCI

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Suna Tinubu, Zai Kashe N900 Biliyan Don Gina Hanyoyi A Najeriya

Dangote
Dangote

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Suna Tinubu, Zai Kashe N900 Biliyan Don Gina Hanyoyi A Najeriya

Daga Sunusi K/Naisa

Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa za a kira hanyar da ke kaiwa zuwa sabuwar matatar mansa da sunan Bola Ahmed Tinubu Road, domin girmama Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wannan taron da aka yi ranar Alhamis, Dangote ya kuma bayyana cewa kamfaninsa zai kashe kusan N900 biliyan don gina manyan hanyoyi a fadin kasar nan.

A Iya Karanta Wanna:Iftula’i: Bafadan Sarki ya rasa ransa a ƙoƙarin hana hawa doki a Jigawa

Daga cikin wadannan, akwai hanyar Deep-Sea Port Access Road da ke hade tashar jiragen ruwa ta Lekki, yankin kasuwanci kyauta, da kuma matatar mai ta Dangote zuwa babbar hanyar Sagamu-Benin.

“Wannan shirin matatar mai, da gaske tunanin ku ne,” in ji Dangote ga Shugaba Tinubu. “Don haka, mun yanke shawarar sanya wa babbar hanyar mu sunan ku – Bola Ahmed Tinubu Road.”

Dangote ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda goyon bayansa ga ‘yan kasuwa, inda ya tuna yadda shugaban ya kafa yankin kasuwanci kyauta a Legas a lokacin da yake gwamna.

A Iya Karanta Wanna:Kungiyar RATTAWU Reshen Jahar Kano na Ta’aziya Ga ‘Yan Wasan da Suka rasu Sanadiyar Haɗarin Mota

A shekarar da ta gabata, kamfanin Dangote ya biya haraji N450 biliyan – wanda ya fi dukkan bankunan Najeriya suka hada jarin harajin da suka biya.

Wannan shiri na gina hanyoyi yana cikin shirye-shiryen gwamnati na ba da rangwamen haraji domin inganta kayayyakin more rayuwa a kasar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...