Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta nuna Fina-finai masu dogon zango 22
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
A ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana’antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai batare da cika ƙa’idar da doka ta tanadar ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma inda ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidan TV
Shugaban Hukumar Alh. Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo ƙarshen ƙorafe korafen da Hukumar take yawan karba dan ƙara inganta aiyukan Hukumar tare da masana’antar kannywood.
Ka Iya Karanta Wanna:Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta Ce Dole A Rage Farashin Burodi, ta Kafa Kwamitin Don Magance Matsalar
Read also: Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in yaɗa labaran Hukumar ya bayyana fina-finai da aka dakatar kamar haka:
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Haka kuma hukumar na sanar da su cewa su mika fina-fina ga hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nan da sati ɗaya mai zuwa wato daga LITININ, 18 ga watan MAYU, 2025 zuwa 25 ga MAYU, 2025 domin gujewa fushin doka.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
A Iya Karanta Wanna:Majalisar Matasan Arewa ta nuna damuwa da matsanancin rashin wutar lantarki a Kano
A karshe Hukumar ta nemi hadinkan dukkannin gidajen TV da Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya wato NBC kan su ci gaba da taimakawa Hukumar domin samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar kannywood.




























