Ramadan
Daga Sunusi Kofarnaisa
Read also: Mutane 16 Gini Ya Faɗawa A Unguwar Dandishe A Kano
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Yusuf ya baiwa wasu daga cikin kungiyoyin Yan jaridu tallafin shinkafa buhu 450
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Alfijir labarai ta ruwaito wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Sanusi Bature D-Tofa ya Sanyawa hannu.

RAMADAN KAREEM
Bature yace kungiyoyin da suka amfana sun haɗar da ƙungiyar ‘ƴan jaridu ta ƙasa reshen jihar (NUJ) da kugiyar Jami’an hulɗa da jama’a ta ƙasa reshen jihar Kano (NIPR) da ƙungiyar mata ƴan jaridu (NAWOJ) da ƙungiyar marubata labarin wasanni reshen jihar Kano (SWAN) sauran su ne ƙungiyar ma’aikatan radio da talavijin da wasan kwaikwayo da kirkirar (RATTAWU) da kugiyar shugabannin kafafen ƴaɗa labarai da kuma ASSOMEG ƙungiyar ‘yan jaridu ta yanar gizo.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
A Karanta Wannan:Gwamnatin Tarayya ta Rage Kuɗin Wankin Koda Zuwa ₦12,000 daga ₦50,000
Raban ya gudana a cibiyar ‘ƴan jaridu dake Farm Center dake jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Comr Ibrahim Abdullahi Waiya da mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature D-Tofa da wakilan kafafen ƴaɗa labarai da Kuma kungiyoyin.




























