Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi da Kwacan Waya: Tayi Holin Wasu Matasa Ga ‘Yanjaridu A Kano

Anti Illicit Drugs....
Anti Illicit Drugs....

Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi da Kwacan Waya: Tayi Holin Wasu Matasa Ga ‘Yanjaridu A Kano

Daga Abdu Ado K/Naisa

Shugaban Hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi gami da kwacan waya na jihar Kano, Brigadiar General Gambo Mai Aduwa (Mai ritaya) yayi holin wasu matasa guda hudu ga manema labarai da hukumar ta kama a kano.

Mai Aduwa ya ce hukumar ta kama matasan a gurare da ban-dabam bisa zargin su da aikata miyagun dabi’u wadanda suka jibanci sha da sayar da miyagun kwayoyi gami da kowacen waya.

A Karanta Wanna:‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya

Kamar yadda yai karin haske, mutum biyu an kama su bisa zargin sai da muggan kwayoyi dakuma tabar wiwi, daya kuma yana sayar da maganin gargajiya wanda aka hadashi da madarar sukudaye da kuma farar kwaya wadda akewa lakabi da( sha fara Kaga Aljan).
Haka kuma shugaban ya ce guda biyu daga cikinsu ana zargin su da kwacan waya, sai dai daya ya barranta kansa da hakan, inda ya ce shi “Dan sane” ne kawai.

A Karanta Wanna:Ƙasurgumin Dan Dabar Da Ya Addabi Jama’a A Kano Burakita Ya Sheka Barzahu
Brigadiar General Gambo ya bukaci iyaye da sauran jama’a da su taimakawa kokarin gwamnatin na magance wanna matsala da ta Addabi al’umma gami da sanar da hukumarsa irin wanna batagari cikin hanzari.

A Karanta Wanna:‘Yar Shekara 35 ta Rasu, ‘ya’yenta Biyu Sun Jikkata Sanadiyar Faduwar Gini a Unguwar Makwarari A Kano
Ya kuma bada tabbacin gabatar da matasan gaban hukuma bayan kammala bincike domin su karbi sakamakon su.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...