Shugaba Tinubu Ya Umarci Kamfanin NNPCL Ta Biya Tallafin Man Fetur
Daga Wakilinmu
Read also: China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar da kamfanin mai na ƙasa, NNPCL ya aike masa na dawo da biyan tallafin man fetur.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa NNPCL ya nemi Tinubu da amince ya biya ribar da ya samu ta 2023 a matsayin tallafin mai a maimakon ya saka kudin a asusun gwamnatin taraiya.
Read also: Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli
Ka karanta wanna:Kwangilar Magunguna: Gwamna Yusuf Ya Ce Bashi Da Masaniya Kuma A Gaggauta Bincike
A rahoton da TheCable ta wallafa a yau Litinin, Tinubu ya bada umarnin ne bayan da NNPCL ya bayyana cewa ƙarar da duk wasu hanyoyi da zai bi ya riƙa samar da daidaito a farashin mai a ƙasar ya faskara.
“Saboda haka Tinubu ya ba NNPCL umarnin amfani da kudin haraji da riba da sauran kuɗaɗe da ya samu wajen biyan tallafin mai maimakon sanya su a asusun gwamnati,” in ji rahoton.
Read also: Shugaba Donald Trump Ya Soke Visa Dubu 80 Ta ‘Yan Najeriya Da Wasu Kasashen Waje
Ka karanta wanna:Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu
Idan za a tuna, shugaban kasa Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sai dai akwai alamun da ke nuna cewar har yanzu gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawa a kan tallafin, zargin da Gwamnatin Tarayya ta sha musantawa.




























