Kwamitin Binciken Hukumar KNUPDA ya Buɗe Kofar Karɓar Korafe-korafe Ko Shawara Game da Hukumar
Daga Adita
Kwamitin jiha mai bincike ayyukan Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) na kira ga jama’a da suke da wani korafi game da ayyukan da KNUPDA ke gudanar wa da su tuntubi kwamitin domin bayyana korafin su.
Kira ya fito daga Shugaban Kwamitin Hon. Dr Dalhatu Aliyu Sani da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Read also: Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
HISBAH A BAUCHI TA HUKUNTA MATASAN DA SUKA DAURA AUREN SADAKIN N3000
Read also: Karamar Hukumar Bichi Za Ta Gina Wa Dagatanta 44 Sabuwar Fada
Shugaban wanda shine Darkta Janaral na hukumar KANGIS ya ce kwamitin ya lura da yawan korafi da al’ummar jihar Kano ke yi bisa hukumar KNUPDA, don haka akwai bukatar masu irin wannan kuka da su bayyana gaban kwamitin da sahihan bayanai domin samar da gyara mai ɗorewa a hukumar.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Dr Sani ya ce za a iya rubuta korafe-korafen da sahihan bayanai da lambar waya da kuma samar da ƙarin hujjoji masu ma’ana ga Sakatariyar Kwamitin Provost Rahama Mallam Alhaji, a Hedikwatar hukumar KNUPDA dake kan Titin Durbin Katsina, Bompai, Kano. Kuma za a rufe karɓar ƙorafe-ƙorafe da takardun shawarwari zuwa Laraba, 1 ga Yuli, 2026.
Idan za a tuna a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin biyo bayan korafe-korafen jama’a game da Hukumar KNUPDA na tursasawa jama’a da zargin yawaitar cin hanci da karɓar rashawa gami da jinkirin rashin aiwatar da ayyukan da suka gabata.



























