Karamar Hukumar Bichi Za Ta Gina Wa Dagatanta 44 Sabuwar Fada
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: Hukumar NDLEA ta Gano Maboyar Miyagun Kwayoyi a Ƙarƙashin Ƙasa a Kano
Majalisar Karamar Hukumar Bichi ta saka dambar gina wa dagatan yankin 44 zaunanniyar fada karkashin sahalewar Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, a yayin hirarsu da Jami’ar Yada Labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo a ofishinsa, jim kadan bayan ganawarsa da dagatai goma da aikin zai fara ta kansu.
Da yake jawabi shugaban karamar hukumar, ya ce, alkawari ne da suka dauka za su cika na gina wa dukkan dagatan Karamar Hukumar Bichi sabuwar fada, sakamakon rashin gyara na tsawon lokaci.
Kazalika da sanin cewa dagatai iyayen kasa ne mafi kusa da jama’a da suke taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar zamantakewar al’umma, ta fuskar samar da zaman lafiya da tsaro kasancewarsu na masu fada a ji a dukkan yankunansu.
Fadar Dagatan da za a fara ganawa su ne: Yola da Doddo da Fagolo da Damarga da Danzabuwa. Sauran fadar akwai ta garin Waire da Kaukau da Huggalawa da Tinki da kuma Tukwibi.
“Waɗannan su ne dagatan da Allah ya sa cikin ikonsa aikin zai fara ta kansu, ko da wane lokaci yanzu za mu je mu fara wannan aiki, ɗan kwangila ya zo kuma Gwamna ya ba mu dama mu je a fara, shi ne dalilin da muka zauna da su yau, mu ka ce su je su yi shiri za mu turo musu ɗan kwangila domin ya zo su ba shi wuri ya fara gabatar da aiki,” inji shugaban Ƙaramar hukumar.
Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ja hankalin takwarorinsa shugabannin ƙananan hukumomi na Kano cewa; su daure su gudanar da irin wannan aiki a kananan hukumominsu, domin hakan zai ƙara danƙon alaƙa da haɗin gwiwar kyautata al’amuran jama’a a tsakaninsu, inda kuma ya yi kira ga dagatan su alkinta fadar idan an yi, ta fuskar kula da tsafta da makamantansu.
“Yana ɗaya daga cikin abin da ya sa muka zauna da su, za a inganta fadar sosai yadda za ta zauna, duk baƙon da za su yi in Allah ya yarda ba za su ji kunya ba, za a fitar da fasali mai kyau yadda kowa in ya zo ya gani za ki ga an ɗauka a jihar Kano baki daya in sha Allahu.”
Dagacin Waire, Alhaji Mustapha Halilu Danwaire da dagacin Fagolo, Malam Habibu Adamu sun nuna farin cikinsu da godiya a madadin dagatan ƙaramar hukumar bisa tagomashin alheri da ba su yi zato ba.
Read also: Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli
Nambobin Wayar Kar-Ta-Kwana Daga Hukumar Yan Sandan Jihar Kano
“Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi; mun tabbata mai girmashugaban ƙaramar hukumar yana da kishin gidaje irin namu na gargajiya.”



























