Connect with us

Hi, what are you looking for?

RA'AYI

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

Sanata Barau Jibril
Sanata Barau Jibril

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

Daga Abba Anwar

Da farkon farawa dai ya kamata mai karatu ya fahimci waye Engineer Abdullahi Garba Ramat. Shi ɗin ya na ɗaya daga cikin tsofaffin shugabannin Ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Mutum ne kam da ya yi karatu mai kyau kuma mutum ne da ya yarda da bin hanyoyin zamani na kimiyya da fasaha dan samarwa al’ummarsa mafita. Ya na ɗaya daga cikin tsoffin shugabannin ƙananan hukumomin da nake girmamawa saboda iliminsa da hangen nesan sa.

Haka nan kuma, shi kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Ƙasa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ya kasance ba baƙon zafi ba ne. Wani tuggu da ɗora masa karan tsana a siyasa da nuna masa ƙiyayya a fili, ba yau ya fara ganin su ba. In har a na sabo da sharrin abokan hulɗa na siyasa, to shi kam ya saba.

Misali ɗaya zuwa biyu kan yadda ya sha baƙar wahala da tsana a baya. Kafin zaɓen 2023, ya taɓa kawo motoci da za a rabawa ƙungiyoyin dalibai na jihar Kano da kuma wasu ƙungiyoyin ma. A nan gidan Gwamnatin jihar Kano a ka ajiye motocin, ɓangaren nan da a ke kira da Coronation Hall.

Kamar yadda ‘yan siyasa suke, idan irin haka ta samu, sai mutum ya sa sunan sa a jikin motocin dan a nuna cewar ga wanda ya bayar da taimakon motocin. To waɗancan motocin shi ma Sanata Barau ya sa sunan sa a motocin gaba ɗaya.

Majalisar Shari’ar Najeriya Ta Nemi Tinubu Ya Cire Shugaban INEC Saboda Wani Rubutu Mai Cike da Cece-kuce Akan “Kisan Kare Dangi”

Abin mamaki sai a ka ce masa ba za a raba motocin ba sai ya goge sunan sa daga jikin motocin. Abinda kuwa ya faru kenan. A ka goge sunan sa a ka sa wani sunan daban. Bawan Allah duk bai ce komai ba.

Ko da a ka zo raba motocin ga waɗancan ‘yan ƙungiyoyin, duk wanda ya tashi yin magana a wajen, ba wanda ya ma ambaci sunan Sanata Barau a wajen, balle ma a nuna cewar shine ya kawo wannan gudunmawa. Abin dai akwai takaici kuma akwai tausayawa.

Ba ma wannan ba, ai bayan an gama taron, saboda tsananin takaici da wulaƙanci da ya gani a wajen, sai da kai ta kawo, wasu daga cikinmu a wajen mun kula da ƙwalla cike da idon Sanata Barau.

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono

To ba ma wannan ba, lokacin zaɓen 2023, ƙemadagas a ka hana Sanatan fom ɗin da zai cike dan nuna sha’awar sa ta tsayawa Sanata. Allah cikin ludufin Sa, sai da Sanatan ya taɓa alli da Abuja sannan ya samu fom ɗin tsayawa takarar.

Dan Allah Ya nuna Shine fa Allah mai yi ba wani abin halitta ba, a haka cikin wannan nuna tsana da tsangwama, Sanatan ya tsaya takara, kuma shi kaɗai ne Sanata ɗan jam’iyyar APC daga Kano da ya ci zaɓen sa. Ragowar Sanatocin guda biyu sun fito ne daga jam’iyyar adawa a lokacin ta NNPP.

Dan dai Allah Ya nuna Shine Allah, kwatsam da a ka shiga majalisa, sai Sanata Barau ya samu nasarar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Allah kenan Buwayi Gagara Misali. Amman abin mamaki duk wannan da ma wasu makamancin hakan har yanzu ba su zama izina ga mutane ba.

Saboda haka abubuwan dake faruwa kan zargi da kage da tsangwama da a ke nunawa Sanatan kan maganar tantance Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC), wai cewar ya yi uwa ya yi makarɓiya kan ganin Ramat bai samu mukamin ba, ba farau ba ga Sanatan.

Kafin ma a je ko ina sai da Babban Daraktan National Productivity Centre, Baffa Babba Dan Agundi ya fito daga baya bayan nan ya yi wani jawabi cewar, wasu mutane sun je sun same shi, kan cewa su haɗa kai da shi a ƙara iza wutar ta hanyar ƙage da sharri.

A cikin jawabin nasa da ya yi, ya ce nan da nan ya yi Allah Wadai ga bukatar waɗannan mutanen. Ya ce shi ba a haɗa baki da shi dan yi wa mutane kage da sharri kan abinda ba su aikata ba. Nan da nan ya fatattaki waɗanda su ka je masa da wannan bukata.

Kuma ya yi kashedin cewa muddin ya ga wannan bukatar tasu ta ɓulla a wani waje, to zai fallasa sunayen mutanen. Ya ce ya tabbatar ba hannun Sanata Barau kan abinda ke faruwa ga Ramat a wannan ƙadamin.

Ya ƙara da cewar kawai a na ɗaukar alhakin Barau ne. Ya kuma ƙara da cewar duk da ba ya goyon bayan Sanata Barau a kan buƙatar sa ta siyasa, amma ya tabbatar an sha yi wa Sanatan irin waɗannan sharrace-sharrace a baya. In da ya ce kuma ya tabbatar Allah ba zai kama Sanata Barau kan abinda bai yi ba.

Daga cikin sharrin da a ke wa Sanata Barau da ma shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio, shine wai “… an ba su cin hancin Dala Milyan Goma ($10m) kan su yi duk yadda za su yi ganin cewa Eng Ramat bai samu kujerar ba.” Babbar magana!

Ban ƙara gane zurfin wannan zargi ba sai da na ga jaridar Daily Trust ta ranar Juma’a, 7 ga watan Nuwamba, 2025, ta ruwaito shugaban kwamitin yaɗa labarai na Majalisar Dattawan, Sanata Yemi Adaramoda ya na cewa,” Wannan zargi ne na banza da wofi.”

Daga nan ya faɗi yadda ma shugaban ƙasa ya turo da sunan Eng Ramat ga majalisar dan neman tantancewa da sahalewarsu wajen ganin ya samu kujerar. Ya kuma yi bayanin irin matakan da a ke bi dan tabbatar da hakan.

Ban fara tunanin cewa waɗanda suke fitowa da sunan wai su na kare Ramat, sun fara haka masa rami ba ba sai da na ji Sanata Adaramoda ya ce, majalisa fa ta karɓi koke masu tarin yawa daga jama’a kan wannan naɗin da a ke son majalisa ta tantance shi. Kuma a dalilin irin waɗannan koke a can baya akwai mutanen da a ka soke samun mukamansu. Ya yi nuni da cewa Ramat ba fa wani shafaffe da mai ba ne da za a banbanta shi da irin waɗancan na baya ba.

Ban kuma kara tsinkewa da al’amarin ba sai da na ji Sanata Adaramoda ya ce, ba fa wani mutum da ya isa ya tilasta majalisa ta yi abinda yake so ba. Daga nan kuma sai ya ce, “Za mu kai ƙarar Alwan kan wannan ƙage da ya yi wa majalisa, dan ya je gaban alƙali ya kawo dalilansa.”

A nasa ɓangaren shi kuma Eng Ramat, daga jin wasu mutane sun fito da wasu maganganu kan wai a na yi masa (Ramat) manaƙisar samun tantancewa da samun wannan matsayi, nan da nan ya fito ya nisanta kansa da irin waɗannan mutanen.

Ya ce “Yanzun nan a ke jan hankali na kan abinda a ke haɗawa cewar wai Sanata Barau ya na ƙoƙarin ganin ban samu tantancewa ba da kuma samun wannan mukamin na shugabancin hukumar NERC. To wannan magana ba haka ba ne ƙarya ne gaba ɗaya ta.”

A takaice ma sai da ya ƙara bayanin irin taimakon da Sanata Barau yake yi masa a kan harkar tun daga lokacin da a ka mika sunan sa a majalisar dan tantancewa.

Babban abin mamaki kuma shine yadda su dai waɗancan mutanen da ke ƙoƙarin danna Ramat a ramin ƙare-kukanka, su ka yi biris da sanarwar da Ramat ya fitar na nesanta kansa da dukkan iƙirarin su, sai su ka ci gaba da baje-hajarsu. Ramat bai yi ƙasa a gwuiwa ba, ya sake fitar da wata sanarwar nesanta kansa da mutanen da kuma dukkan iƙirarin su gaba ɗaya.

Ya sake cewa, “Waɗannan maganganun fa da a ke haɗa ni da su, kan zargin Sanata Barau da Sanata Akpabio, ban san su ba. Kuma ba da yawu na a ke yin su ba.” Ya ƙara jaddada irin goyon bayan da yake samu daga Sanata Barau da ma dukkan Sanatocin da su ka fito daga jihar Kano.

Cikin fushi sai da ya nuna cewar, matsawar mutanen da ke baza wannan ruɗu da ƙage da sharri da sunan su na son sa ne, to fa idan tura ta kai bango zai iya neman haƙƙin sa a kotu. Ya dai ƙara nisanta kan sa da waɗancan mutanen da suke nuna wai su masoyan sa ne.

Tun farkon farawa a nasa ɓangaren wani mutum da a ke kira da Alwan Hassan daga ƙaramar hukumar Nassarawa, a Kano, dan tsohuwar jam’iyyar nan ta CPC, wacce ta haɗu da wasu jam’iyyu wajen kafa jam’iyyar APC, har kiran taron manema labarai ya yi ya na ta baza rudɗu da hayaniya da sharri ga Sanata Barau.

Ya kamata mai karatu ya tuna da cewar, su fa ‘yan bangaren CPC da ke cikin APC, sune ɓangaren da su ka nuna kiyayyarsu ga takarar Bola Ahmed Tinubu tun ma kafin ya samu sahalewar jam’iyyar APC a zaben 2023. Kowa ya san yadda su ka nuna ƙiyayyarsu ga takarar shugaba Tinubi tun daga farkon farawa. Amma da yake Allah ne ke bayarwa, sai ga shi Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kuma fa su ‘yan tsagin CPC sun yaƙi jam’iyyar APC katitur da Tinubu ya samu takara a 2023. Sun yaƙi jam’iyyar ne tun daga can sama har ƙasa zuwa jihohi. Sai nake mamakin yau idan wani ɗan CPC ya fito ya ce wai shi ko ita masoyin gwamnatin Tinubu ne. Abin dariya, wai yaro ya tsinci haƙori.

A cikin sambatun wancan mutumin wai shi Alwan, har fa cewa yake wai Sanata Barau makiyin Kano ne da yan Kano. Da na ji haka na kasa fahimtar me ma yake nufi. Kalli irin dubban ɗaliban da Sanata Barau yake ɗaukar nauyin karatunsu a jami’o’inmu na cikin gida. Da kuma waɗanda ya tura zuwa ƙasashen waje dan karo ilimi a matakin karatun Digiri na biyu. Shi a wajen Alwan duk wannan ba shine kishin Kano ba ne.

Kalli fa irin ƙoƙarin da Barau ya yi wajen kafa hukumar raya arewa maso yamma, wato North West Development Commission, kalli jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kabo da Sanata Barau ya yi ƙoƙarin samarwa. Ga kuma makarantar Federal College of Education, Kano, wacce bayan an mayar da ita University lokacin shugaba Goodluck Jonathan, lokacin Malam Ibrahim Shekarau yana Ministan Ilimi, amma da shugaba Buhari ya zo ya cire matsayin University da a ka ba makarantar. Amman da Tinubu ya zo, sai da Sanata Barau ya sake ƙoƙarin ganin an sake dawowa da makarantar muƙaminta na University.

Kuma a ka sa wa makarantar sunan Dan Masanin Kano, Yusuf Maitama Sule University of Education, Kano. Duk ta hanyar ƙoƙarin Sanata Barau. Ga kuma tallafin motocin aiki da babura da Sanatan yake ba wa hukumar ‘yan sanda ta ƙasa, reshen jihar Kano. Amman a wajen Alwan duk waɗannan abubuwan ba kishin Kano ba ne.

Na ƙalubalanci Alwan da ya zo mana da wasu abubuwan ci gaba da raya al’umma da ya kawowa mutanensa, iyakacin tsukin mazabarsa kawai, daga lokacin da a ka ba shi mukamin mataimaki na musamman ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Prof Yemi Osinbajo, har zuwa lokacin da ya gama.

Wani babban abin dariya da ƙyaƙyacewa shine da shi wannan mutum Alwan yake wani haƙiƙicewa wai ba za su bar Barau ya zama gwamnan jihar Kano ba shekarar zabe ta 2027. Wallahi abin ya mugun ba ni dariya sai da na kusa fadowa daga kan kujera.

Dan Allah ku gane min hanya, wai mutumin da ko mazabar sa ba ya ci balle ƙaramar hukumar sa wai shine zai bugi ƙirji ya ce wai zai hana wani samun muƙamin gwamna. shawara

Ni kuwa zan ba Sanata Barau cewar ya turo da wakilansa su zo su samu Alwan su durkusa su roƙe shi, su ce masa dan Allah Ya yi haƙuri ya taimaki Sanatan ya zama gwamnan Kano a 2027. Hahahahahaha. Abin dariya abin ƙyaƙyacewa hahahahaha.

Ni fa abinda nake gani shine, su yan tsagin CPC a cikin APC sun koma yin kame-kame ne a wannan gwamnatin ta Tinubu dan neman gindin zama. Amman har yanzu sun kasa gane cewar shi fa Tinubu idonsa a buɗe yake ba makaho ba ne. Kuma har yanzu har gobe ya na iya tuna muguwar wahalar da ya sha a hannun ‘yan CPC a 2023.

Ɗalubai Sun Hallaka Malaminsu A Sanadiyar Chacha

Ya kamata Alwan ya fahimci cewar idan fa ma neman gindin zama yake to ya mugun makara. Kuma ina son ƙara tuna masa cewar, idan nufin sa ya samu ta cewa a siyasar Kano, to shi ma a nan bai yi tunani mai kyau ba. Ni dai har yanzu ban ga wata hanyar da Alwan zai bi ya zama wata tsiya ba a siyasar Kano. Wutsiyar Rakumi tai mugun yin nesa da ƙasa!

Ina kuma son tunasar da masu karatu cewar, ita fa ƙifificewa da shafa toka a fuska da cin zarafin shugabanni ba a keɓanta su ga wasu gungun jama’a ba. Kowa ma ya na iya yi. Kai hatta mahaukaci a kan titi zai iya. Tun da ai ɗabi’u ne da ba sa buƙatar wata ƙwarewa ko wata gogewa ta rayuwa.

Anwar ya rubuto wannan daga Kano, Talata, 11 ga watan Nuwamba, 2025

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...