Nijeriya Kasarmu Ta Gado Mai Wuyar Zama
Daga Dr A.M Tahir Kofar Na’isa
Read also: Yarjejeniyar Zaman Lafiya da Alero: Gaskiya Ko Wasan Kwaikwayo Da Rayukan Al’umma
Haɗin-gambiza da haɗin-gwarman da Turawan Mulkin Mallaka su ka yi wa wannan ƙasa wadda su ka kira ta Nijeriya, tabbas, sun san, ba su yi tsarin da za’a zauna lafiya ba.
Haka kuma duk masu hankali a cikin wannan ƙasar da wajen ta, sun san cewar tsarin ba mai ɗorewaba ne. Sannan, kuma kawo tsarin siyasar Turai bai dace da asalin tsarin rayuwar wannan al’ummar ba, wanda a cikinsa, ƙuri’ar mai hankali da mara hankali da kuma ta mai ilmi da jahili da gogagge da karabuti, wanda bai ma san abin da ya ke yi ba, wai duka darajarsu ɗaya ce. Marasa hangen nesan da su ka fi yawa, wai su ne za su zaba wa al’umma makoma mai kyau. Ana sani aka jefa rayuwar mutane cikin tasku da takaici da sunan wai siyasa! Wannan matsala ce, da babu wanda ya san ranar fita daga cikinta, sai Allah.
‘Yan kudancin wannan ƙasa, su na ɗaukar ‘yan Arewaci tamkar ba mutane ba, su na nuna musu mahaukaciyar ƙiyayyar da babu gaira – babu – dalili. A gefe ɗaya kuma ‘Yan Arewacin ƙasar ta Najeriya na yanzu da shugabaninsu da talakawansu, tamkar ba mutane ba, sun zamanto sai son duniya da famkama da baƙin jahilcin yadda siyasar duniya ta ke gudana shi ya mamaye zukatansu.
Ka Iya Karanta Wanna:Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko
Misali, a baya-bayan nan matsalar da a ka samu a jihar Edo, da a ka yiwa mutanan Arewa kisan gilla, masana sun ce: “Ba wannan ne farau ba”. Anan, yana da kyau, ‘yan kudancin Najeriya mazauna Arewa, su nuna damuwarsu, ko da a ƙalla ta hanyar zanga – zangar lumana ne, domin su barranta kansu da abin da ya faru, gami da nuna ƙyama ga mutanensu da suka yi wannan aika-aika. Lashakka yin hakan zai taimaka gaya wajen kaucewa ɗaukar doka a hannu.
Read also: Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat
Ko da yake shugabannin su sun ziyarci jihar Kano tare da yin godo gami da ban hakuri da kuma neman afuwa ga shugabanninmu da kuma ahalin wanda waƙi’ar ta faɗawa, toh, anan zamu iya cewa son barka. Su kuma da suka rugayemu muna rokon Allah ya kyautata makwanci.
Kuma ina kira ga ragowar shugabanninmu na Nijeriya da ke kallon abu da idon basira, su daure su sama wa ƙasar nan mafita ta gari, ko da kuwa hakan ba zai yi wa wasu daɗi ba, idan kuma ta kai a raba ƙasar kamar yadda wasu ke iƙirari to a raba ta cikin hanyar lumana da tabbatar da zaman lafiya, ba sai mun afka irin ta makotan mu ba kamar ƙasar Sudan da makamantansu, Allah ya kiyaye.
Haka kuma ina roƙon manyan malamanmu na addini da ilmi da siyasa da masana tattalin arziki, da su haɗu a tebur guda tare da ajiye banbance-bambancen su guri guda domin “Karatun ta nutsu” a kan al’amuran da su ke gudana a ƙasar nan don sama wa kasar alƙibila ta gari.
Ka Iya Karanta Wanna:Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno
Read also: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA MAI GIRMA ƊAN MAJALISAR TARAYYA, MAZABAR GWALE
“Wallahi! Tarihi ba ya afuwa, kuma ba zai manta da duk abin da ya faru ba, duk daren daɗewa sai ya zaƙulo ya kuma bayyana duk abubuwan da su ka gudana, ko muna da rai ko ma ba ma raye. Mu yi fatan bar wa ‘ya’yanmu kyakkyawan tarihi ba mummuna ba.”
Na ku Dr Kofar Nai’sa, A.M.Tahir -Mai yi wa Najeriya fatan alheri.




























