Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono

'Yan bindiga
'Yan bindiga

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono
Daga Wakilinmu

‘Yan bindiga sun kai hari a ƙauyen ‘Yan Kwada da ke karkashin yankin Faruruwa, ƙaramar hukumar Shanono a Jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar ciki har da masu shayarwa. Shaidar gani da ido, daga yankin ta ce maharan sun isa garin wajen karfe biyar na yamma ne da tarin yawa, ɗauke da makamai, suka shiga gidaje suna harbe-harbe da tsoratar da mutanen gari, kafin su tafi da wadanda suka kama.

Ɗalubai Sun Hallaka Malaminsu A Sanadiyar Chacha

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wadannan mata biyar, biyu sun Allah ya kwato su sun kubuta sun koma gidajensu, yayin da sauran uku har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutanen.
Wannan harin ya zo ne mako guda bayan rundunar haɗin gwiwa ta sojoji ta yi artabu da ‘yan bindigar a yankin, inda aka kashe mutum 19 daga cikinsu.

Mazauna Faruruwa da wasu kauyuka makusanta da ke kan iyakar Kano da Katsina sun dade suna fuskantar hare-hare masu maimaituwa, wanda hakan ya jefa su cikin fargaba da tashin hankali. Saboda tsanani da yawaitar hare-haren, wasu kauyuka sun tarwatsa sun bar garuruwan nasu, jama’a suna kaura zuwa Faruruwa ko kuma garuruwa na cikin birane don neman tsira da rai.

Ana Zargin Fashewar Bam A Masallacin Juma’a Yai Sanadiyar Jikata Daruruwan Mutane a Yau

A gefe guda, al’umma da shugabannin yankin na ci gaba da rokon gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakin gaggawa, domin magance wannan matsala da ta jima tana addabar rayuwar jama’a da tattalin arzikin kauyukan yankin da ma kasar Arewa gaba ɗaya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...