Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

MA’AIKATA 4 NA MATATAR RUWAN GUBI DAM, BAUCHI SUN RASU A BAKIN AIKI

Bauchi State
Bauchi State

MA’AIKATA 4 NA MATATAR RUWAN GUBI DAM, BAUCHI SUN RASU A BAKIN AIKI

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Bauchi- Mutane hudu da ke aiki a madatsar ruwa ta Gubi dam da ke bayar da ruwan sha a ciki da wajen garin Bauchi sun rasu a lokacin da suke tsaka da aikin tsambtace matatar da hanyoyin da ke tura ruwan zuwa garin Bauchi da kewaye.
Cikin sanarwar rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar CSP Mohammed Ahmed Wakil a madadin kwamishinan ‘yan sanda Sani Omolori Aliyu ta bayyana cewa a ranar Lahdi 20/4/2025 da misalin karfe biyar na yamma sun samu labarin makalewar mutanen hudu a cikin matatar, yadda cikin hanzari suka isa suka taras mutanen hudu sun rasu.

Sanarwar ta bayyana cewa sun fara aikin ne tun daga misalin 12 na Rana yadda daga bisani aka samu akasin rashin rufe wani sashen bututun tura ruwa lamarin da ya haifar da iftula’i da ya hallaka mutanen hudu.

A Iya Karanta Wanna:Mutane 148 sun mutu a wani haɗarin kwale-kwale da ya faru a Congo

Wanda suka rasu sun haɗar da Shayibu Hamza Mai shekara 48 da Abdulmalik Yahaya Mai shekara 29 da Jamilu Inusa shekara 29 da Ibrahim Musa mai shekara 42 dukkan su mazauna garin Firo a karamar hukumar Ganjuwa mazaunin matatar ruwan ta Gubi dam.

A Iya Karanta Wanna:Al’ummar Unguwar Lokon Makera A Kano Sun Koka da Kamfar Wutar Lantarki

Rundunar ‘yan sandan da hukumar samar da ruwa ta jihar Bauchi sun mika sakon taziyya ga iyalai da ‘yan uwa da abokan aikin wadanda suka rasu, Kuma sun bayyana ci gaba da bincike kan lamarin tare da daukar dukkan matakan da suka dace na ganin irin hakan bai sake faruwa ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...