Mutane 148 sun mutu a wani haɗarin kwale-kwale da ya faru a Congo
Aƙalla mutane 148 aka tabbatar da sun mutu a wata gobara da ta tashi a cikin jirgin ruwa can a yankin arewa maso yammacin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Read also: Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
Rahotanni sun ce jirgin wanda na katako ne na ɗauke da fasinja aƙalla 500 kuma kamawar wutar ne ya haddasa masa kifewa a cikin teku, inda yanzu haka an iya ciro gawarwakin mutane 148 yayinda aka iya tseratar da wasu 100 da ransu, kodayake akwai ɗimbin waɗanda suka ɓace a ruwa.
A cewar bayanai jirgin mai suna HB Kongolo ya kama da wuta ne a gab da ƙauyen Mbandaka bayan tasowa daga tashar jiragen ruwa ta Matankumu da ke lardin Bolomba.
A Karanta Wanna:Al’ummar Unguwar Lokon Makera A Kano Sun Koka da Kamfar Wutar Lantarki
Shugaban tashar jiragen ruwan Competent Loyoko ya shaidawa manema labarai cewa wutar ta tashi ne, sakamakon girki da wata mata ke yi a cikin jirgin, kuma ganin wutar ya sanya ɗimbin ƙananan yara da mata faɗawa cikin ruwa ba tare da sanin yadda ake iyo ba.
Read also: Ambaliya ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
Wasu ganau sun ce kaso mai yawa na fasinjan jirgin Mata ne da ƙananan yara, inda yanzu haka ɗaruruwansu suka ɓace a cikin ruwa duk da cewa jami’an agaji sun ce suna aiki tuƙuri don gano gawarwakinsu.
Tuni dai aka gaggauta miƙa waɗanda suka tsira da rayukansu ga wani sansanin wucin gadi don samun kulawar gaggawa.
Haɗarin kwale-kwale ba sabon abu ba ne a Congo, ƙasar da tsaffin jiragen ruwa da aka samar daga katako ke matsayin babbar hanyar zirga-zirgar jama’a musamman a yankunan ruwa.
A Karanta Wanna:LALATA:YAN SANDA NA TUHUMAR MAHAIFI DA YI WA YARSA CIKI A JIHAR BAUCHI
Read also: Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
Ko a bara mutane 78 suka nutse a ruwa lokacin da wani jirgi ɗauke da fasinja 278 ya kife a lardin Kivu na gabashin ƙasar yayinda wani haɗarin na daban kuma ya hallaka mutane 22 lokacin da suma jirginsu ya kife a yammacin ƙasar cikin watan Disamban bara.
rfi




























