Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Al’ummar Unguwar Lokon Makera A Kano Sun Koka da Kamfar Wutar Lantarki

Mal. Dauda Lokon Makera
Mal. Dauda Lokon Makera

Al’ummar Unguwar Lokon Makera A Kano Sun Koka da Kamfar Wutar Lantarki

Daga Sunusi K/Na’isa

Mazauna unguwar Lokon Makera a yankin karamar hukumar Gwale dake cikin kwaryar Birnin Kano sun koka kan yadda suka shafe sama da kwanaki 33 batare da samun wutar Lantarki ba duk da kasancewar su a cikin kwaryar Birnin Kano.

Malaman Addinin musulunci a yankin Malam Dauda Muhammad lokon Makera ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Shahararen Malamin ya ce abin takaici ne yadda mutanen yankin suke fama da matsanancin rashin wuta lantarki tun cikin Azumin watan Ramadan har zuwa yanzu duk da kasancewar su cikin kwaryar Birnin Kano kuma suna kokarin biyan kuɗin wuta a duk wata.

A Karanta Wanna:LALATA:YAN SANDA NA TUHUMAR MAHAIFI DA YI WA YARSA CIKI A JIHAR BAUCHI

Alhaji Dauda ya yi zargin nuna halin ko-in-kula daga shugabanni yankin musamman ‘yan siyasa da suka hadar da ‘Yan majalisar tarayya da na majalisar dokokin Jihar Kano, ya na mai cewa “mafi yawan al’umma ba su ma san wadanda ke wakiltarsu a yankin ba kuma cikinsu harda ni duk da kasancewata malamin Addinin musulunci kuma dan boko”.

Dauda lokon Makera ya bukaci kamfanin rarraba hasken wutar Lantarki na jihohin Kano da Jigawa da Katsina KEDCO da ya kaiwa al’ummar yankin dauki.

A Karanta Wanna:Iftula’i: Mata biyu sun haɗu da ajalisnsu sakamakon Faɗawa Kudiddifi A Kano

Inda ya ce matukar ‘yan siyasa a Gwale suka gaza warware matsalolin da mutane ke fama da su akwai ranar kin dillanci, ranar da kowanne dan siyasa zai je da bukata kuma al’ummar su yi watsi da bukatarsa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...