Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Hukumar Shari’ah da kungiyar Wamy sun shiryawa waɗanda suka karbi Musulunci shan ruwa a Kano

Hukumar Shari'a da WAMY sun hada taron iftar
Hukumar Shari'a da WAMY sun hada taron iftar

Hukumar Shari’ah da kungiyar Wamy sun shiryawa waɗanda suka karbi Musulunci shan ruwa a Kano

Sunusi Kofarnaisa

Hukumar Shari’ah da haɗin guiwar kungiyar World Assembly of Muslim Youth (Wamy) sun shiryawa waɗanda suka karbi addinin Musulunci tarin shan ruwa a ranar Lahadi da ta gabata a harabar hukumar karkashin Jagorancin Mukaddashin Shugaban Sheikh Ali Danabba.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Darktan Wayar da Kai na Hukumar Shari’a ya sanyawa hannu Malam Musa A Ibrahim (Best Seller) ya ce Shugaban hukumar Shari’a Sheikh Ali Danabba ya bada tabbacin gudanar da irina wanna taro na Shan ruwa da wadanda suka karbi musilinci a duk ranar 15 ga watan Ramadan.

Sheikh Ali Danabba ya kuma mika godiya ga gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf da Kungiyar World Assembly of Muslim Youth [WAMY] da suka basu gudummawa wajen shirya wannan taro.

Hakazalika shan ruwa ya sami halartar dukkanin shugabanin hukumar da suka gabata da mambobinta da kuma ma’aikatanta tare da shugabannin kungiyar Wamy da wasu manyan mutane.

A Karanta Wanna:Gwamnatin Kano ta karrama Hazikan Gasar karatun Alkur’ani

Wakilin shugaban kungiyar Wamy Alh Sanusi ya nuna jin dadinsa da yadda aka gudanar da taron shan ruwa, kuma ya tabbatar da cewar kungiyar su ƙungiya ce ta taimakon addinin musulunci da musulmi a ko ina suke, kuma kungiyar zata ci gaba da wannan aikin alherin da izinin Allah.

Daga cikin wadanda suka rabauta da addinin musulunci, A’isha Suraj tace sun ji dadin yadda ake karrama su da kuma yadda mutane suke jansu a jiki babu nuna banbanci ko kyama “Lalle addinin Musulunci addini ne na gaskiya,” inji Aisha.

Shugaban hukumar Dr Sani Ashir ya godewa Allah da kuma kira ga masu hannu da shuni da su kawowa wadannan yara tallafi domin kara karfafarsu akan addini, sannan kuma ya bada tabbacin cewar wannan shirin an yi shi ne a kurarran lokaci amma ya ci alwashin shekara mai zuwa da yardar Allah shirin zai Zama na musamman kuma abin koyi.

A Karanta Wanna:Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

A jawabinsa Kwamishina na daya a Hukumar Shari’a Gwani Hadi yayi kira ga al’umma da su zo domin Neman auren ‘yan matan da suka karbi addinin Musilinci, gami da tabbatar da kyaykyawar dabi’ar yaran da kuma nagartar su, ya kuma yi addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan jihar da kasa baki daya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...