KUNGIYAR AfriHub TA JAGORANCI BIKIN RANAR MATA TA DUNIYA A BAUCHI
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Za a Fara Jigilar Alhazan Jihar Bauchi Daga Ranar 7 Ga Watan Mayu
Kasancewar majalisar ɗinkin duniya ta ware kowace ranar 8 ga watan Maris a matsayin ranar mata ta duniya, kungiyar Afrihub Mai samun tallafin Plan International da Global Affairs Canada ta gudanar da gangamin wayar da kan Jama’a don kare hakkin mata da inganta rayuwar su a makarantu da yadda suke zaune da iyalansu.
Dr. Saba’atu Danladi Elizabeth Daraktar kungiyar Afrihub a Nijeriya ita ne ta jagoranci gangamin a Bauchi.
Yadda ta ja hankalin gwamnati da Jama’a su taimaka wa mata don su ƙara inganta rayuwar su don martaba al’umma ta hanyar rainon ‘ya’ya da za su taso a yi alfahari da su wajen gina ƙasa da kishin al’umma.
Saba’atu Danladi ta ƙara da cewa ranace ta karrama mata saboda idan hankalin mata ya kwanta a cikin gida dole hankalin maigida da yara ya kwanta, amma idan mata ba su da kwanciyar hankali dole hankalin gida ya tashi.
A Karanta Wanna:Gwamnatin Tarayya ta Rage Kuɗin Wankin Koda Zuwa ₦12,000 daga ₦50,000
Read also: GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA SOKE TAKARDUN FILAYEN KIWO DA AKA RABAWA MANOMA A DARAZO
Don haka ta buƙaci mata idan zabe ya zo, su zabi mata ‘Yan uwan su. Saboda haka idan mace ta samu matsayi ta fi martaba mata ‘yan uwanta da suka zo ganin ta. Saboda wulaƙanta mata da ‘Yan uwan su mata ke yi idan suna riƙe da matsayi shi ke haifar da idan mata sun fito siyasa mata ba sa zabar su.
Hajiya Halima Dimis shugabar ƙungiyar inganta rayuwar mata ta HILWA a Bauchi ta roƙi hukumomi su riƙa bayar da matsayi wa mata don samun muƙamai da za su bayar da gudummowa wajen gina ƙasa da jama’arta.
Don haka ta ce a cikin majalisar dokokin jihar Bauchi babu mace, amma a majalisar zartaswa Gwamna Bala ya sa mata, a ƙananan hukumomi ko ina akwai mata har da Kansiloli. Don haka ta buƙaci mata su tashi su nemi na kansu don tsira da mutuncin su da na iyalan su.
A Karanta Wanna:Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Itama shugabar ƙungiyar mata ‘Yan jaridu ta jihar Bauchi NAWOJ Hajiya Rashida Yusuf ta ja hankalin mata ‘Yan jarida kan su ci gaba da wayar da kan mata game da yadda za su inganta rayuwar su ta hanyar neman abin kan su don samun inganta rayuwarsu da ta iyalan su don a samu raguwar rasa rayuka a cikin gidaje sakamakon rashin fahimta da ake samu a cikin gidaje.
Read also: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Ƙaddamar da Hasken Solar a Dajin Yankari
Tace abin takaici ne a cikin gidaje kasa da mako guda miji ya kashe matarsa mata ta kashe kishiyarta yaro ya kashe iyayensa abun takaici ne.
Don haka ta bukaci mata Yan jarida su inganta salon su na wayar da kan Jama’a game da inganta zaman lafiya a tsakanin iyalai.



























