Daga Wakilinmu
Hukumar hisbah ta jihar Kano ta ce Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne Babban Kwamanda na hisbah a kano har izuwa wannan lokaci, kuma babu wani labarin maganar sauka daga kujerar sa ko makamancin hakan.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Hukumar ta tabbatar wa da wakilinmu ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Alh. Lawan Ibrahim Fagge, inda ya ce har yanzu kwamanda shi ne shugaban hisbah tare da ƙaryata labarin saukar sa daga kujera.
” Yanzu maganar da nake da kai, Kwamanda yana ofis kuma yanzu ma za mu karɓi baƙi bisa jagorincinsa, mu a saninmu bai bar aiki ba kuma babu wanna magana.
A karanata wanna: Ƴar Tik Tok Ta Yi Ɓatan Dabo: Al’ummar Kano Na Ce-Ce-Kuce Kan Sharuɗɗan Beli
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
“Da yake ƙarin haske game da maganar Murja Kunya, ya ce hukumar hisbah ta yi nata aiki. Maganar sakin ta ko akasin haka ba za su ce komai ba domin a saninsu an kaita kotu kuma kutun ta kaita ajiya gidan gyaran hali tare da bada wa’adin sati guda a koma kotun. Saboda haka sai ajira kotun zuwa wannan wa’adi da za a koma”, inji Lawan Fagge.
Raɗe-raɗin saukar kwamandan hisbah ta yamutsa hazo a cikin gari da kafafen sadarwa na zamani da kuma guraren hira da kasuwani da ma’aikatun gwamnati, wanda da yawa sun dangarta hasahen saukar bisa zargin ɓatan dabon da shaharariyar ƴar tik tok Murja Ibrahim Kunya ta yi, ko sama ko ƙasa bayan an gabatar da ita a kotu a satin da ya gabata.
A inda wasu ke zargin masu ido da kwalli ne suka- shiga- suka- fita, har ta samu ƴanci daga gidan gyaran halin da aka kai ta ba tare da koma wa kotun ba, ballantana ace beli aka bayar.
A karanata wanna: Tsadar Rayuwa: “Ku Fito Da Kayan Abinci, Ko Mu Farke Rumbunan Mu Siyarwa Da Jama’a”, Inji Muhyi Rimin Gado
Idan an tuna, jami’an hukumar Hisba ta jihar Kano su suka kama mashahuriyar ƴar TikToke ɗin, sakamakon zarginta da yaɗa bidiyon baɗala a shafinta na sada zumunta da kuma zargi tana ƙoƙarin lalata tarbiyar ƴaƴen maƙotanta wanda ake ganin ya saɓa wa tanade-tanaden shari’ar musulunci ta jihar Kano ta shekarar 2000.




























Pingback: Ƙungiya ta Gargadi Majalisar Kano kan Rushe Sabbin Masarautu - The StentorNews Hausa