Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙuduri aniyar ɗorawa a kan nasarorin da magabata suka samu wajen magance ƙalubalen da almajiri da yaran da ba sa zuwa makaranta ke fuskanta a fadin kasar.
A ziyarar girmamawa da ya kai ofishin PRNigeria da ke Abuja, Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Almajiri da Yaran da ba sa zuwa Makaranta, Hon. Sha’aban Sharaɗa, ya bayyana shirye-shiryen gabatar da shirin karatun boko, dabarun sana’o’i, da sauran ayyuka masu amfani ga almajirai miliyan 20 da yaran da ba sa zuwa makaranta a shekarar 2027.
Read also: China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
Sharaɗa ya jaddada cewa, “ƙarfin almajirci da yaran da ba sa zuwa makaranta da ke da ƙwarewar koyon sana’o’in hannu na iya share fagen makoma mai haske, yana taimakawa wajen kyautata tattalin arzikinsu da zamantakewarsu. Abubuwan da muka fi mayar da hankali a kai sun haɗa da linkin keke da yin tufafi da noma da kiwon kaji da sarrafa abinci da dabarun adana shi. Sauran sun haɗar da kiwon kifi da kamun kifi da koyar da sarafa fatu da ƙiraga da sauransu.”
Ya kuma bayyana aniyar Hukumar na shirya taron tunawa da almajirai da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta da za a yi a Najeriya, tare da goyon bayan da gwamnatin jihar Sokoto da gwamnonin arewa suka yi alƙawari, da kuma shugabannin gargajiya da na addini.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Sharaɗa ya bayyana cewa, “Mun yi la’akari da ƙoƙarin da aka yi a baya kuma mun gano rashin wani wa’adin da tsarin mulki ya ba mu a matsayin cikas. Tare da ƙudirin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu, yanzu muna da goyon bayan da ya kamata a fannin shari’a, don tabbatar da nasarar da muka sanya gaba.”
A jawabinsa, Babban Jami’in Kamfanin Hotuna na Promotion Limited (IMPR), Mista Yushau Shuaib, ya yaba wa Hon. Sha’aban saboda jajircewarsa wajen magance kalubalen da yaran da ba sa zuwa makaranta ke fuskanta, yana mai nuna ƙwarin gwiwa kan iyawarsa na yin tasiri mai kyau tare da goyon bayan dukkan masu ruwa da tsaki




























