Connect with us

Hi, what are you looking for?

KASUWANCI

Abokan Ciniki da Dillalai Sun Jinjina wa Ɗangote bisa Tallafinsa don Bunƙasa Kasuwancinsu

DSC7814
DSC7814

Daga S A K/Na’isa

A bokan hurɗa sun bayyana cewa tausayi da karamcin Ɗangote ne suka sanya ya tsere wa tsara a harkokin kasuwanci a Najeriya da kuma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Da suke bayanin a yayin bikin karrama abokan hurɗa da kamfanin simintin Ɗangote na shekarar 2023 da aka gudanar a karshen mako a Legas, abokan hurdan waɗanda suka fito daga ko’ina a faɗin kasar nan, sun bayyana dangantakar kasuwancinsu da kamfanin Ɗangote a matsayin ‘kyakkyawar alaka’ da mai ƙaunar ganin abokin hurɗa ya cigaba.

A lokacin bikin dai an raba wa dillalai kyaututtuka masu gwabi saboda imanin da suka yi da kamfanin siminti na Ɗangote ta hanyar ci gaba da sayen kayayyakinsa.

Baya ga mawaka irin su Kizz Daniel da Tuface Idibia da suka cashe don nishalantar da baƙi a lokacin bikin, akwai kuma waɗansu fitattatun manyan Najeriya da suka halarci bikin domin taya Ɗangote da abokan hurdar Kamfanin murna.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarta akwai, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi da shugaban kamfanin Geregu Power, Femi Otedola da kuma tsohon ministan Masana’antu da Ciniki da harkar zuba jari, Otunba Niyi Adebayo da sauran manyan baƙi da dama.

Kamfanin Kazab Heritage ne ya samu kyautar dillali na shekara, a yayin da kamfanin Gilbert Igweka Global Concept, ya zo na biyu, kamfanin Nwa Ado Resources Nigeria ya zo na uku.

Waɗanda suka samu nasara daga yankunan ƙasar nan kuwa, sun haɗar da Kamfanin Twins Faja Enterprises, wanda ya zo na ɗaya a yankin Legas/Ogun, sai Nwa Ado Resources Nigeria da ya zo na ɗaya a yankin Arewa ta tsakiya, sai kuma Abdullahi Fugu, da ya zo na ɗaya a yankin Arewa Maso Gabas, akwai kuma Giwa Dynamis Ventures, da ya zo na ɗaya a yankin Arewa Maso Yamma da kuma D.C.Okika Nigeria Limited wanda ya zo na ɗaya a yankin Kudu Maso Gabas.

A cewar shugaban kamfanin Twins Faja Nigeria Limited Mista Wale Fajana, ‘ na kwashe fiye da shekara 20 ina dillancin simintin kamfanin Ɗangote, kuma tun daga lokacin harkar kasuwancina take habaka kamar wutar daji.”

Ya bayyana cewa, ya fara harka da kamfanin Ɗangote ne tun kamfanin yana Apapa, kuma tun daga lokacin ‘
Ya ce, shi da abokan cinikinsa sun yi matukar amfana da kamfanin siminti na Ɗangote a cikin shekaru masu yawa da suke hulda da shi.

Shi kuwa Alhaji Abdullahi Fugu na A.A.Fugu &Sons, wanda yake zaune a yankin Arewa Maso Gabas na Najeriya, cewa ya yi, ya fara hulda da kamfanin siminti na Ɗangote ne da karamin jari, amma saboda taimako da goyon bayan da ya samu a wurin Ɗangote da kuma jami’an gudanarwar kamfanin, yanzu ya zama babban dillali na kayan kamfanin. Ya kara da cewa, “Alhaji Ɗangote mai karimci ne sosai, shawarwarinsa sun taimaka wajen bunƙasa kasuwancina. Kuma kamfanin ya taimaka wa dillalansa sun daukaka harkarsu, kuma ya ɗauki mutane aiki.” a cewar Fugu.

A nasa bangaren, shugaban kamfanin Nwa Ado Multi Biz, Cif Akukalia Igwebuike, wanda yana cikin manyan diloli guda uku, ya alakanta nasarar da ya samu ne a kan goyon bayan da ya samu daga kamfanin Ɗangote, musamman Aliko Ɗangote, wanda ya ce ya yi ƙoƙari ƙwarai wajen ganin kasuwancinsa ya bunƙasa, kuma a kowane lokaci yana ba shi shawara domin cigaban harkar kasuwancinsa. “Babu abin da zan ce sai godiya ga Alhaji, saboda taimakawar da ya yi wa harkar kasuwancina. Don haka na yi alƙawarin ƙara jajircewa a wannan shekara ta 2024 domin in tashi daga matsayin na uku zuwa matsayi na gaba a cikin dillalan kamfanin.”

A nata jawabin, Misis Beatricr Chinwe Okika, shugabar D.C.Okika Nigeria Ltd, wacce babbar dilaliya ce a yankin Kudu Maso Gabas, cewa ta yi, alaƙarta da Dangote ta wuce ta kasuwanci, ‘ domin tun daga lokacin da mijina ya rasu Ɗangote yake taimaka mun tare da kasuwancina.”

“A kowane lokaci yana kulawa da iyalina da kasuwancina, yana kuma taimakawa da kudi da bayar da taimako iri-iri domin taimaka wa iyali da kasuwancina, taimakon da Dangote yake mini ba ya kidayuwa.”

A cewarta, kamfanin siminti na Ɗangote yana cigaba da taimaka wa duk dillalansa domin kara danƙon alaƙarsu. Allah Ya akbarkace shi, Ya kuma cigaba da yi masa jagora.”

Shi ma Injiniya Festus Abononkhua na kamfanin Raybale Nigeria Ltd, bayyana Ɗangote ya yi da cewa abokin huldar kasuwanci ne mai nagarta.

Ya ce, da farko a matsayinsa na Injiniya har kunya yake ji a ga yana dillancin siminti, amma yanzu yana matukar alfahari da kasancewa dilalin simintin Dangote.

Ya ƙara da cewa, a yau da taimakon kamfanin simintin Ɗangote harkar kasuwancinsa ta bunƙasa sosai a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...