Mai baiwa gwamnan kano shawara akan kasuwanci Hon. Nura Husaini (president) ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, murna bisa gaggarumar nasarar da ya samu a kutun ƙoli.
Ya ce wannan nasara ce ta al’ummar jihar Kano idan akai la’akari da manyan ayyukan da mai girma gwamna ya bujiro dasu domin ci gaban al’umma da bunƙasa jihar Kano baki ɗaya.
Read also: Ko Kasan Sabbin Kwamishinonin Da Gwamna Kano Abba Yusuf Ya Naɗa?
Nura Hussaini ya furta hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin STENTORNEWS a Kano, ya ce irin wannan ayyukan da gwamna Abba Kabir ya ɗako cikin wata bakwai kawai yafi na gwamnatocin da suka huce acikin shekaru takwas.
Read also: Ka Daina Siyasartar Da Harakar Tsaro, Barau Jibrin Ya Gargaɗi Gwamna Kano
Don haka ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su ci gaba da yi wa mai girma addu’a da kuma bada goyon baya don samun ci gaban jihar Kano,
Da ya juya ɓangaran Yan kasuwa Hon. Nura Husaini, ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin Kawo ƙarshen matsalolin da suke addabar ƴan kasuwar Jihar Kano nan bada jimawaba. Haka kuma gwamnati na shirin fito da wasu shirye-shirye a manyan kasuwanin jihar nan ta yadda za su dace da zamani nan bada jimawa ba.




























