Farfesa Pantami Ya Samu Nasara A Sabon Zaɓen Ɗan Takarar Gwamnan Gombe A PDP
Daga Sunusi K/Naisa
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaɓen ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe a Jam’iyyar PDP.
Shehin Malamin addinin Musulunci, Isa Ali Pantami ya samu nasara a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda ya doke sauran ’yan takarar da suka fafata da shi a zaɓen.
Read also: BASHI NA DAF DA DURKUSAR DA NAJERIYA
Kotun Tarayya a Gombe Ta Soke Zaben da Aka Yiwa Farfesa Isa Ali Pantami
Khamisu Ahmed Mailantarki ne ya zo na biyu yayin da Usman Aliyu Garry ya zo na uku. An gudanar da sabon zaɓen ne a yau Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe, wadda ta soke zaɓen fidda gwani na farko da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Read also: Tsohon Gwamna Jigawa Sule Lamido Ya ce Zasu Samawa Jam’iyyar PDP Mafita Kwanana
An Sace Sarki da Ɗan Kasuwa da Mutane 13 a Alkaleri, In ji Galan Gwana
Ina za a tuna Kotun ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani cikin wa’adin da ta ƙayyade, bisa dokokin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokar zaɓe.




























