DOKTA IBRAHIM WAZIRI BAUCHI YA FITO TAKARAR SHUGABAN KASA A APM DON DAWO DA TALLAFIN MAI DA INGANTA TSARO.
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Read also: INEC: Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa Na Zaɓen Shekarar 2027
Dan takarar shugaban kasar Nigeria a jamiyyar APM Dr. Ibrahim Waziri Sarkin Sullubawan Bauchi ya bayyana magance matsalar talauci a tsakanin jamaar Kasa Shi ne zai kawo karshen taaddanci da ake fama da shi a Nigeria.
Ibrahim Waziri Sarkin Sullubawa ya bayyana haka ne a lokacin da ya kira taron manema labarai a Bauchi don bayyana kudirinsa na yunkurin ceto mutane daga wahala da shugabanni suka jefa su.
Ya Kara da cewa abin takaicine a kowane lokaci Yan Nigeria suna yin zabe don su huta amma a kullum zababbun da aka zaba ba su damu da shawo kan matsalolin da suka damu talakawa ba.
Don haka Dokta Waziri ya ce wannan shine Karo na uku da ya fito takarar shugaban Kasa don bayar da gudummowar ceto talakawa a Nigeria a karkashin jamiyyarsa ta APM. Kuma tuni ya rubuta takardun bayyana bukatarsa ga uwar jamiyyar a Abuja har sau hudu amma ba su ba shi amsaba. Kasancewar sa tsohon dan siyasa kuma dan gwagwarmayar da ya jima yana karatu da ayyuka a kasashen duniya, shine ya yanki katin jamiyyar APM kuma ya bayyana aniyar sa a idon duniya.
Read also: Farfesa Pantami Ya Samu Nasara A Sabon Zaɓen Ɗan Takarar Gwamnan Gombe A PDP
HISBAH A BAUCHI TA HUKUNTA MATASAN DA SUKA DAURA AUREN SADAKIN N3000
Musamman ganin yadda talaucin da aka kallafawa mutane ya fatattaka rayuwar Yan Kasa ya haifar da matsalar da Allah kadai ya san ranar fita daga ciki, don haka azzaluman shugabanni basa kaunar taimako ga talakawa, sai Yan gwagwarmayar kawo sauyi sun tashi tsaye kafin a samu gyara a fagen siyasar Nigeria.
Yace dawo da tallafin man fetir da dangoginsa da inganta harken lantarki da samar da ayyukan yi sune zai fara tunkara idan ya nasarar zama shugaban kasa a Nigeria don a samu fita daga mawuyacin halin da ake ciki.
Har wa yau Dr. Ibrahim Waziri Sarkin Sullubawan ya bayyana cewa a halin da ake ciki, na ci gaban sadarwa irin ta zamani dukkan shugaban da ya kudiri aniyar gina mutanen sa da ciyar da su gaba, zai yi nasara ba tare da bata lokaci ba. Kuma zai inganta rayuwa ta hanyar bayar da ilmi da kiwon lafiya kyauta don a share hanyar inganta zaman lafiya da tsaron mutanen Kasa.
Yace Nigeria Kasa ce da ta mallaki tattalin arziki Kala Kala tun daga man fetir da iskar gas da maadinan cikin Kasa da noma da kiwo da mashigin ruwa da kasuwanci a cikin kasa da wajen ta da filayen jiragen sama da sufurin jirgin ruwa da layukan sadarwa na wayoyin salula da yawan mutane masu basira da sauran hanyoyin samun kudin shiga, amma an gaza ci gaba kullum sai wahala da kashe kashe da cutar da mutanen Kasa.
Don haka ya ce abu na farko da zai tunkara shine a rage kaifin talauci da wahala tsakanin mutane ta hanyar dawo da tallafin man fetir da dangoginsa da kuma inganta hasken lantarki da rage kudin wuta.
Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Ya Faɗa Komar EFCC
Don haka ya ce wajibi ne idan ya samu shugabancin Nigeria kowa zai gani a kasa kamar yadda ake da komai a Kasa amma komai ya fi karfin mutane za a basira da zai nuna don ceto mutanen wannan kasa.




























