Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar Abduljabar, ta umurci a hanzarta sauraron shari’ar a Babbar Kotun Kano
Daga Sunusi K/Naisa
Kotun Ɗaukaka Ƙara, reshen Kano, ta kori ƙarar da Abduljabar Nasir Kabara ya shigar bisa dalilin rashin inganci, sannan ta mayar da shari’ar ga Babban Alƙalin Jihar Kano domin a hanzarta sauraron ta bisa maslahar adalci.
Read also: Kotun Kano Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa Sau Bakwai Kowanne Saboda Kashe Mace Da Yara Shida
Mai ƙara (Appellant) ya shigar da ƙarofinsa a Kotun Ɗaukaka Ƙara ne domin neman a duba masa hukunci.
An same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a watan Disamba 2022 a Kotun Shari’ar Musulunci ta Ƙwali ta Jihar Kano, bayan an same shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Lokacin da aka ci gaba da sauraron shari’ar a yau Alhamis, mai ƙarar ya roƙi kotu ta ba shi damar gabatar da kansa ba tare da taimakon lauya ba.
A martaninsa, lauyan gwamnatin Jihar Kano (wanda ake ƙara), Bashir Saleh, Daraktan Rubuta Dokoki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, ya sanar da kotu cewa ya riga ya miƙa wa mai ƙarar takardar ƙin amincewa ta farko (Notice of Preliminary Objection) jiya, inda ya ƙalubalanci dukkanin ƙarar.
Ga Wasu Labarun:
Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar
Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Abduljabbar Ya BuƙaciƊauka ka Ƙara A Babbar Kotu, Kano
Read also: Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓen Kano, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
Lauyan ya yi hujjar cewa ƙarar da Mallam Abduljabar ya shigar tana da matsala domin kotun ƙasa ba ta yanke wani hukunci ko yanke shawara a kan shari’ar ba.
Ya bayyana cewa har yanzu shari’ar na gudana a Babbar Kotun Kano (Sashin Ɗaukaka Ƙara) a gaban Mai Shari’a Amina Adamu, inda kawai ta ɗage shari’ar ba tare da sanya ranar ci gaba ba domin ba Mallam Abduljabar damar samun lauya.
Sale ya ƙara da cewa buƙatarsa ta dogara ne da tanadin Dokar Kotu, Sashi na 19.
A hukuncinsa, Alƙalin da ya jagoranci zaman, Mai Shari’a Muhammed Lawal Shuaibu, ya ce bayan nazari mai zurfi kan bayanan da ɓangarorin biyu suka gabatar, kotu ta tabbatar cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara kotu ce mai tattara shari’o’i, kuma duk takardar da za a gabatar a gabanta dole ne ta bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa na gudanar da aikinta.
Don haka ya ce ƙarar Abduljabar ba ta da inganci saboda ba a bi ƙa’idojin kotu ba.
Alƙalin ya kuma shawarci Mallam Abduljabar da ya nemi taimakon lauya, yana mai cewa shari’arsa ta shafi hukuncin kisa kuma tana buƙatar ƙwararren lauya.
Kotun ta kuma bayyana cewa takardar ƙin amincewa ta farko da lauyan wanda ake ƙara ya gabatar, wadda ke ƙalubalantar hurumin kotu kan ƙarar, ba ta da cikakken inganci duba da cewa shari’ar na ci gaba a kotun ƙasa.
“Kotun ƙasa ta yi kuskuren doka da ta ɗage shari’ar ba tare da sanya ranar ci gaba ba. Kotun Ɗaukaka Ƙara na iya sauraron ƙara ne kawai idan akwai hukunci ko yanke shawara daga kotun ƙasa. Wannan ƙara ba ta da inganci domin babu hukuncin da aka yanke daga kotun ƙasa da zai ba mu damar sauraron ta.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Dangane da haka, mun kori wannan ƙara saboda rashin inganci.
Sai dai kuma, bisa la’akari da yanayin ƙarar da kuma maslahar adalci gaba ɗaya, an mayar da shari’ar ga Babban Alƙalin Jihar Kano domin a hanzarta sauraron ta.
Ya kamata ka koma kotun ƙasa ka kammala dukkan matakan shari’ar kafin ka dawo nan neman a sake duba maka hukunci, in ji Alƙali.
Ba ma gudanar da sabon sauraro ƙara ba ne, muna duba hukuncin kotun ƙasa ne kawai,” in ji kotun.





























Pingback: Kotun Tarayya a Gombe Ta Soke Zaben da Aka Yiwa Farfesa Isa Ali Pantami - The StentorNews Hausa