An Yi Kira ga Karamar Hukumar Sumaila da ta Samar da Bandaki a Makarantar Liman Yau JASS Sumaila.
Daga Sunusi K/Naisa
Shugabar makarantar Liman Yau Junior Arabic Secondary School dake karamar hukumar Sumaila, Malama Bilkisu Suleiman Yusuf, ce ta yi kira ga shugabancin karamar hukumar da ta taimaka wajen samar da bandaki a makarantar domin inganta tsafta, lafiya da walwalar dalibai da malamai.
Malama Bilkisu ta bayyana cewa rashin isashen bandaki na iya janyo matsaloli da dama, musamman wajen tsafta da lafiyar dalibai, lamarin da ke iya kawo cikas ga harkokin koyo da koyarwa da a makarantar.
Read also: Karamar Hukumar Ghari Ta Raba Takardun Daukar Aiki Ga Malamai 50
An Kama Umar Da Wasu Matasa 2 Da Ake Zargi da Kashe Matar Aure Da ‘Ya’yenta 6 A Kano
Kamar yadda Jami’in yada labarai na
Karamar Hukumar Sumaila ,Murtala Umar kawo ya ruwaito Shugabar ta ce mafi yawa idan buƙata kewayawa ta kama yaran sai dai su shiga maƙotansu ko kuma su koma gidajensu.
A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Sumaila, Alhaji Farouk Abdu Sumaila, ya bayyana cewa gwamnati na samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa a makarantu, tare da jaddada kudirinta na ci gaba da tallafa wa bangaren ilimi.
Read also: Hukumar KAROTA Zata Samar Da Motocin Sufuri Ga Ɗaliban Jami’ar Sule Lamido Dake Jigawa
SUBEB DA UNICEF DA UBEC SUN KADDAMAR DA GANGAMIN SA YARA MAKARANTA A BAUCHI
Shugaban ya ƙara da cewa karamar hukumar za ta duba wannan buƙatar samar da banɗakuna cikin gaggawa domin ɗaukar matakan da suka dace, domin tabbatar da cewa dalibai na samun ingantaccen yanayi na karatu da rayuwa a makarantar, Ya kuma yi kira ga shugabannin makarantu da al’umma gaba ɗaya da su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai domin samun ci gaba mai ɗorewa a bangaren ilimi.



























