Gwamnan Kano Abba Yusuf Ya Umarci ‘Yan sanda su Gaggauta Kamo Waɗanda Sukai Kisan Gilla A Unguwar Dorayi
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana baƙin cikinsa kan kisan gillar da akai wa wata mata da ‘ya’yanta a unguwar Dorayi Chiranchi. Ina da ya bayyana al’amarin da rashin hankali da tsantsar wulakanta martabar Dan Adam.
Gwamna ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da haka ta hannu Babban Darkta mai lura da harkar Sadarwa Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa da ya fitar a ranar Asabar.
Abba Kabir Yusuf, ya mika ta’aziyarsa ga iyalan mamatan da al’umma Dorayi Charanci da jama’ar jihar Kano baki daya.
Read also: Rundunar Ƴan sanda ta Hana Goyo a Babur a Kano
An bukaci al’umar karamar hukumar Rano da su kara marawa kokarin gwamnatin jiha Kano na bunkasa harkokin ilmi.
Gwamnan ya umarci ‘yan sanda su gaggauta kamo wadanda suka aikata kisan, Yana mai cewa duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci fushin doka.
Kisan Gillar Uromi: Iyalan Mafarautan Kano da Aka Hallaka A Edo Sun Fara Fidda Rai Da Adalci, Ƙungiyoyi Na Shirin Zanga-Zanga
Ya kuma nemi dakarun rundunar tsaron Jihar su maida hankali wajen yin sintiri a guraren da ake samun tarzoma a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa tsaron jama’a. Ya kuma buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu tare da baiwa hukumomin tsaro haɗin kai wajen sanar da duk abinda basu yarda da shi ba.



























