Zancen Teburin Mai Shayi: Waye Kai Da Zaka Ce A Janye ‘Yan Sanda daga Nassarawa, Aminu Babba ya Kalubalanci Kwankwaso
Daga Edita
Read also: Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda
Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya kalubalanci tsohon Gwamna jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso bisa kalamin da yayi na cewa Sarki ɗaya ne a Kano kuma a janye jami’an tsaro daga gidan Sarki na Nassarawa, “Kai waye da zakace a Janyewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Jam’ian Tsaro baka isa ba kuma baka da iko.
Sarkin Dawaki Babba ya sanar da haka ne a sanarwar manema labarai da aka sanya hannu daga Kakakin Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Abubakar Balarabe Kofar Naisa a yau Talata.
Ya ce Kwankwaso bashi da wani Hurumi na bada Shawarar Janye Jami’an tsaron a Gidan Sarki na Nassarawa.
NBA Ta Bukaci a Dakatar da Dokar Gyaran Haraji Saboda Kuskurewa Bin Tsarin Doka
Alhaji Aminu Babba Dan Agundi yace Maganar da take kotu to Kai waye zakayi wannan maganar a Matsayin kanawa, in ji shi.
Alhaji Aminu Babba Ya ce Kwankwaso bashi da wani Hurumi akan wannan, kuma koshi Gwamnan Kano Alhaji Abba Yusuf bashi da wannan damar, domin maganar tana gaban kotu.
Sarkin Dawaki Babba ya kara da cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kotu ce ta bashi wannan tsaro ba Gwamnati ba.
Don haka ne ma ya ce wannan maganar da Rabiu Musa Kwankwaso yayi daidai take da zancen Teburin Mai sayar da shayi.
Read also: Kimanin ‘Yan Jaridu 29 Yakin Hamas da Isra’ila Ya Lakume Ya Zuwa Wannan Lokaci
’Yan Najeriya 42 Aka Kora Daga Ƙasar Ghana Sakamakon Karuwanci da Aikata Miyagun Ɗabi’u
Babban ɗan Majalisar Sarkin Sarkin ya ce idan kwankwaso bai fahimta ba ya Kamata ya gane cewa irinsu da basu da mukamin komi aka ce a Janyewa Jami’an ‘Yan Sanda.




























