Daga Abdul M. Hotoro
‘Yan jarida 29 aka kashe a yakin da Isra’ila ke yi da Palasdin kuma shi ne mafi muni a kisan ‘yan jarida a kowane irin yaki cikin kankanin lokaci.
Tun bayan harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma hare-haren ramuwar-gayya da Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza, an kashe ‘yan jarida aƙalla 29 a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta ta kwamitin kare ‘yan jarida (CPJ).
Adadin ƴan jaridar da aka kashe ya haɗa da Falasdinawa 24, da ƴan Isra’ila hudu da kuma ɗan jarida daya ɗan ƙasar Lebanon, daga lokacin harin farko har zuwa ranar 29 ga watan Oktoba.
Doaa Sharaf, ‘yar jarida ce ta gidan rediyon Al-Aqsa mai alaƙa da Hamas, an kashe ta a ranar 26 ga watan Oktoba, tare da ɗanta, a wani harin da Isra’ila ta kai a gidanta da ke Yarmouk a birnin Gaza.
Ɗaya daga cikin abokan Doaa ta ce tana da “murmushi mai sanyaya zuciya”.
An kashe Salma Mkhaimer, ‘yar jarida mai zaman kanta mai shekaru 31 a ranar 25 ga Oktoba, tare da jaririnta da mahaifinta da mahaifiyarta da kuma wasu ‘yan uwa da dama, a wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Rafah. Tana zaune ne a Jordan amma ta koma Gaza don ziyarar iyali ta ba-zata kafin ɓarkewar rikicin.
Read also: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Bulla A Nijeriya
Muhammad Imad Lobbad, mai shekaru 27, ɗan jarida ne na shafin yaɗa labarai na Al-Resalah, kuma an kashe shi a ranar 23 ga watan Oktoba a wani harin da Isra’ila ta kai a unguwar Sheikh Radwan a birnin Gaza.
Rushdi Siraj, mai shekara 31, shi ne ya kafa kamfanin Ain Media, wani kamfani na Falasdinwa da ya ƙware kan ayyukan yaɗa labarai.
An kashe shi ne a ranar 23 ga watan Oktoba a wani hari da Isra’ila ta kai a Gaza.
Ya bar mata ɗaya da ɗiya ƴar ƙasa da shekara ɗaya. Abokan aikinsa sun ce: “Mun yi rashin babban mutum, amma Rushdi ya koya mana mu ma.”
Khalil Abu Atherah wani mai ɗaukar hoto ne na gidan talabijin na Al-Aqsa mai alaƙa da Hamas. An kashe shi tare da ɗan uwansa a ranar 19 ga watan Oktoba a wani harin da Isra’ila ta kai a Rafah da ke kudancin Gaza. Ɗaya daga cikin abokansa ne ya yada hotonsa a Facebook ya ce: “A sauka lafiya Khalil, Allah Ya kiyaye… Ba mu kuma san wanda za mu yi jimami a cikin abokanka ba.”
Sameeh al-Nadi, mai shekaru 55, ɗan jarida ne kuma daraktan gidan talabijin na Al-Aqsa mai alaƙa da Hamas. An kashe shi ne a ranar 18 ga watan Oktoba a wani harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza. Ƴarsa ta ce: “Kawuna, da ma a ce zan iya sake jin muryarka, ina matukar kewar ka.”
An kashe Issam Abdallah, ɗan jaridan bidiyo na kamfanin dillancin labarai na Reuters mazaunin birnin Beirut a kudancin ƙasar Lebanon lokacin da makamai masu linzami da aka harba daga ɓangaren Isra’ila suka tashi da shi tare da jikkata wasu mutane shida. Wasu gungun ‘yan jarida na aiki a kusa da Alma al-Shaab, kusa da kan iyakar Isra’ila, inda sojojin Isra’ila da dakarun sa-kai na Hizbullah suka yi musayar wuta a kan iyakar ƙasar. Isra’ila ta ce ana gudanar da bincike kan lamarin.
Haka kuma CPJ tana bin diddigin adadin ‘yan jarida da suka ɓace ko suka jikkata.
Ya jaddada cewa ‘yan jarida “fararen hula ne da ke yin ayyuka masu muhimmanci” kuma “dole ne bangarorin da ke rikici su guji kai masu hari”.
“‘Yan jarida a duk faɗin yankin suna yin sadaukarwa sosai don kawo rahotanni kan wannan rikici mai ratsa zuciya,” in ji Sherif Mansour, mai kula da shirin na CPJ na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
“Wadanda ke Gaza, musamman, sun sadaukar da rayukan su, kuma suna ci gaba da sadaukarwa, adadin da ba a taɓa gani ba kuma suna fuskantar barazana. Mutane da yawa suna rasa abokan aiki, iyalai, da na’urorin yada labarai, kuma sun gudu don neman mafaka lokacin da babu mafita ko mafaka.”
ABM-BBC




























