Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

’Yan Najeriya 42 Aka Kora Daga Ƙasar Ghana Sakamakon Karuwanci da Aikata Miyagun Ɗabi’u

Karuwanci
Karuwanci

’Yan Najeriya 42 Aka Kora Daga Ƙasar Ghana Sakamakon Karuwanci da Aikata Miyagun Dabi’u

Daga Yazid Sunusi Yahaya

Aƙalla ’yan Najeriya 42 ne aka kora daga yankin Ashanti na ƙasar Ghana bisa zargin aikata karuwanci da damfara, da sauran laifuka masu alaƙa da haka.
Ministan Yankin Ashanti, Frank Amoakohene, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce korar ta biyo bayan hukuncin kotu da aka yanke kan ’yan ƙasashen wajen da abin ya shafa.

A cewar Amoakohene, waɗanda aka kora sun haɗar da ’yan Kamaru 13, ’yan Ivory Coast uku, ’yan Burkina Faso uku, da ’yan Jamhuriyar Benin bakwai, baya ga ’yan Najeriya 42.

Tsohon Ma’aikacin Gwamnati a Kano da Ya Bayar da ₦5m Dukkan Garatitunsa Domin Gina Masallacin Jumu’a Ya Rasu Yana da Shekaru 96

Ya bayyana cewa kotuna sun same mutane waɗanda suka haɗar da maza da mata kuma laifukan da suka aikata sun haɗar da karuwanci da sauran ayyukan laifi, wanda hakan ya haifar da korarsu daga ƙasar.

Ministan ya ce gaba ɗayansu ’yan Afirka 68 ne hukuncin kotunan ya shafa, yana mai jaddada ƙudurin hukumomin Ghana na aiwatar da doka da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Amoakohene ya rubuta cewa:
“Jimillar ’yan Najeriya 42, ’yan Kamaru 13, ’yan Ivory Coast uku, ’yan Burkina Faso uku, da ’yan Jamhuriyar Benin bakwai aka kora daga Yankin Ashanti zuwa ƙasashensu na asali, sakamakon hukuncin kotu daban-daban da suka shafi Q-Net, karuwanci, da sauran ayyukan laifi.”
Ya yabawa gwamnatin Ghana bisa ƙwarewa da jajircewa da tsayayyiyar aniyar aiwatar da dokokin shige da fice na ƙasar.

“Ina yabawa Hukumar Shige da Ficen Ghana bisa ƙwarewarsu da jajircewarsu, da ƙudurin da suke da shi na aiwatar da dokokin shige da fice, tare da mutunta ka’idojin shari’a da martabar ɗan Adam.
“Hadin gwiwarsu da kotuna da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da ƙarfafa tsaron jama’a da kare masu rauni da kuma tabbatar da doka da oda a yankin,” in ji shi.

Korarrar ’yan Najeriya daga Ghana na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotanni na tsaurara matakai na tsaro da kama ’yan Najeriya a ƙasashen waje. A cewar wani rahoto daga kamfanin dillancin labarai na Indiya, NDTV, kimanin ’yan Najeriya 50 ne aka kama a lokacin wani gagarumin samame da aka gudanar a watan Nuwamba, wanda ke daga cikin manyan matakan da Indiya ta ɗauka kan hanyoyin magance safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa-da-ƙasa.

Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano
Ana zargin waɗanda aka kama suna da alaƙa da wata babbar ƙungiyar rarraba miyagun ƙwayoyi da wanke kuɗi ta hanyar danfara, wadda ke aiki a manyan biranen Indiya da dama. Rundunar ’Yan Sanda ta Delhi ce ta jagoranci aikin tare da haɗin gwiwar sashen EAGLE na ’Yan Sandan Jihar Telangana.

Ya bayyana cewa sun sami rahotonin sirri ne a watanni da suka gabata, gami da kai samamen a lokaci guda a sassa daban-daban na Delhi, lamarin da ya bai wa jami’an tsaro damar tarwatsa muhimman sassan wata ƙungiyar safarar methamphetamine da cocaine a faɗin Indiya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...