Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf

One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano

Daga Sunusi K/Naisa

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na aiwatar da Ajandar Kano bai Ɗaya (One Kano Agenda), yana mai bayyana cewa haɗin kai da ɗaukar nauyin alhaki tare su ne ginshiƙan dawo da martabar jihar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya tabbatar da cewa shirin zai ci gaba da samun cikakken goyon baya da haɗin gwiwa daga gwamnatin jihar. Ya bayyana cewa halin da ake ciki a yanzu na buƙatar haɗin kai tsakanin al’ummar Kano, ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, zamantakewa ko al’adu ba.

Ya buƙaci al’ummar jihar da su waiwayi matsayin Kano shekaru arba’in zuwa hamsin da suka gabata, lokacin da jihar ta kasance abin koyi a fannin ilimi, kasuwanci, noma, bunƙasa cigaban matasa, kyawawan ɗabi’u na al’adu da kuma ƙarfafa cibiyoyin gargajiya da suka ja hankalin ƙasa baki ɗaya.

Sule Lamido Ya Yi Gargaɗi Jam’iyyar PDP Na Iya ƙuɗɗa Ƙawance Idan Shugabanci Ya Gaza Warware Rikici

A cewarsa, dawo da matsayinta na tarihi na buƙatar ganganko da haɗin gwiwar kowa da kowa a dukkan sassan al’umma. Ya ƙara da cewa haɗin kai zai taka muhimmiyar rawa wajen fuskantar manyan ƙalubale kamar shan miyagun ƙwayoyi, tare da inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunƙasar arziki ga kowa a jihar.

SSG ɗin ya bayyana cewa gwamnatin NNPP ta cika kusan kashi 85 cikin 100 na alƙawuran da ta ɗauka a lokacin kamfen, yana mai tabbatar da cewa sauran kashi 15 cikin 100 za a kammala su a kan lokaci. Ya kuma bayyana cewa gabanin zangon zaɓe na 2027, gwamnati na shirin sabunta tare da faɗaɗa alkawuran ci gaba domin tabbatar da Kano mai albarka.

A jawabinsa, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi sadaukarwa da jajircewa wajen aikin gina jihar Kano gaba ɗaya. Ya jaddada ƙudirin gwamnati na tallafa wa dattijai da ‘yan fansho da suka sadaukar da rayuwarsu wajen ci gaban Kano.

Kwamishinan ya kuma sanar da shirin miƙa irin wannan tallafi ga tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da suka yi aiki tsakanin shekarun 2014 zuwa 2023, domin girmama gudummawar da suka bayar.

Taron tattaunawar masu ruwa da tsaki ya samu halartar ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran ƙungiyoyi daban-daban, inda aka mayar da hankali kan ci gaban Kano da dabarun magance ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziƙin jihar.

Tun da farko, Shugaban Ƙungiyar one-Kano Agenda, Ambasada Abdullahi Yakasai, ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin dawo da martabar jihar Kano, ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa ba.

Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a sauya munanan ɗabi’u tare da fuskantar ayyukan waɗanda ya kira maƙiyan Kano da suka dagula fannoni daban-daban, ciki har da siyasa, tattalin arziƙi da tsaro. Ya jaddada buƙatar matasa su haɗa kai wajen tunkarar waɗannan ƙalubale domin dawo da tsohuwar martabar Kano.

Rashin Bawa Mata da Kanana Yara Damar Zuwa Asibiti Domin Rigakafi Illa ne Ga Rayuwar Su, In ji Jami’in Lafiya

An gudanar da shirin a Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu, Kano, (KHAIRUN), inda aka fara taron a ranar Larabanan, kuma ana sa ran za a ƙare shi a ranar Alhamis.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...